Sarki Sanusi II Ya Kammala Digirin Digirgir, Ya Samu PhD da Rigimar Sarauta Ta Lafa

Sarki Sanusi II Ya Kammala Digirin Digirgir, Ya Samu PhD da Rigimar Sarauta Ta Lafa

  • Bayan rikicin masarauta a Kano, Sarki Muhammadu Sanusi II ya kara zurfafa iliminsa na zamani a jami'ar SOAS da ke birnin Landan
  • Sarkin a yanzu haka ya kammala digirin digirgir a fannin shari'ar addinin musulunci, inda ya gama ba tare da an ci gyaransa ba
  • An gano mai martaba sarki Sanusi a wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya na bayyana farin cikinsa na samun PhD

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

London, UK - Sarkin Kano, mai martaba Muhammadu Sunusi II ya kammala karatunsa a fannin shari'ar addinin musulunci a birnin Landan.

Sarkin ya kammala bincikensa na gama karatun a kan yadda za a yi amfani da dokokin iyali na addinin musulunci wajen daidaita rayuwar jama'a.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II na shirin zama Dakta, babu kuskure a kundin binciken da ya rubuta

Sarki
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya kammala digiri na 3 a Landan Hoto: Sanusi II Dynasty
Asali: Facebook

Sa'adatu Baba Ahmad ta wallafa a shafinta na Facebook cewa Sarkin ya yi bincike kan amfani da shari'ar a masarautar Kano tare da kwatanta shi da na masarautar Morocco.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bidiyon da ta wallafa, an gano Sarkin ya na murna yayin da aka tabbatar masa bincikensa ba ya bukatar wani gyara.

Yaushe Sarkin Kano ya fara karatun?

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa sarki Muhammadu Sunusi II ya fara karatun ne bayan gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta tsige shi daga karagarsa a 2020.

Kafin ya koma karatun, Sarki Sanusi ya yi kokarin kawo sauyi a zamantakewar auren bahaushe a masarautar inda ya rika fadan wasu hakkoki na mata a musulunci.

Sarki Sanusi ya samu ilimi a fanni daban-daban, daga cikinsu akwai digiri na biyu a fannin addinin musulunci da fikihu daga jami'ar Africa International University Khartoum, Sudan.

Kara karanta wannan

Miyagu na yi wa jami'an tsaro dauki ɗai ɗai, an kona wani har gida a Katsina

Sarki Sanusi II ya koka kan illar zanga-zanga

A wani labarin kun ji cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sunusi II ya ziyarci wasu daga cikin wuraren da masu zanga-zanga su ka lalata a Kano.

Mai Martaba Muhammadu Sanusi ya bayyana bacin rai kan yadda jami'an tsaro su ka yi sakaci har masu zanga-zanga su ka rika lalata muhimman wurare.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.