Mutane Kusan 20 Sun Mutu Yayin da Sojoji Suka Yi Gumurzu da Ƴan Bindiga a Arewa
- Ƴan bindiga aƙalla 15 sun baƙunci lahira da suka yi gumurzu da dakarun sojoji a ƙaramar hukumar Wase da ke jihar Filato
- Mazauna yankin kauyen Gudiri sun ce lamarin ya faru ne lokacin da sojoji da ƴan banga suka kai samame maɓoyar ƴan bindiga ranar Litinin
- Wani ɗan banga ya ce sojoji uku sun rasa rayukansu a musayar wutar amma an kashe ƴan bindiga sama da 15
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau - Ƴan bindiga da dama sun bakunci lahira a wata musayar wuta da suka yi da sojoji a kauyen Gudiri da ke ƙaramar hukumar Wase a jihar Filato.
Hakan na zuwa ne kwanaki biyu bayan da sojoji sun gano gawar dan sandan da aka yi garkuwa da shi ranar Larabar makon jiya a kusa da kauyen Kampani da ke yankin Wase.
Mazauna yankin sun shaidawa Daily Trust cewa an yi musayar wutar tsakanin jami'an tsaro da ƴan bindiga ranar Litinin da ta gabata da yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda sojoji suka farwa ƴan bindiga
A cewarsu, sojoji tare da haɗin guiwar ƴan banga sun kai samame sansanin ƴan bindigar dajin bayan samun bayanan sirri kan yawan hare-hare a yankin.
Mutanen da ke rayuwa a yankin sun kara da cewa jami’an tsaro sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar daga maboyarsu.
Jami'an tsaron sun kwato shanu sama da 100 waɗanda ake zargin ƴan bindigar sun sace su ne a hare-haren da suka kai.
Mai magana da yawun Operation Save Haven, rundunar tsaron da ke aikin wanzar da zaman lafiya a jihar Filato, Manjo Samson Zhakom, bai ɗaga kira ba.
'Sojoji 3, yan bindiga 15 suka mutu'
Shapi’i Sambo, shugaban matasa a Wase ya ce duk da bai san adadin wadanda suka mutu a artabun ba amma sojojin sun kashe ƴan bindiga da dama, Punch ta kawo.
Wani ɗan banga da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:
"Yanzu muka dawo daga wurin, ina daga cikin waɗanda suka jagoranci sojoji zuwa wurin. Sojoji uku suka mutu yayin da ƴan bindiga sama da 15 suka bakunci lahira."
Plateau: An kashe shugaban matasan fulani
A wani rahoton kuma kun ji cewa 'yan bindiga sun hallaka shugaban matasa na kungiyar Miyetti Allah a jihar Plateau.
Marigayin mai suna Yakubu Muhammad ya rasa ransa ne a karamar hukumar Bassa da ke jihar a Arewa ta Tsakiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng