Yan Bindiga Sun Harbe Sarkin Gobir, Sun Rike Dansa a Daji
- Rahotanni na nuni da cewa yan bindiga da suka yi garkuwa da Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa sun harbe shi har lahira a daji
- Magajin garin Gobir, Shuaibu Gwanda Gobir ya tabbatar da cewa a yammacin ranar Talata ne yan bindigar suka halaka sarkin
- Sarkin Gobir ya fito a wani bidiyo yana rokon gwamnatin jihar Sokoto kan ta biya masa kudin fansa domin ya samu kubuta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Yan bindiga sun harbe mai martaba sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa bayan sun yi garkuwa da shi.
Yan bindigar sun kashe sarkin ne kwanaki kadan bayan ya fito yana neman a biya masa kudin fansa.
BBC Hausa ta wallafa cewa a yanzu haka ana ƙoƙarin ƙubutar da dansa, Kabiru Isa da aka sace su tare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kama Sarkin Gobir
Wani dan sarkin ya bayyana cewa yan bindiga sun yi kwanton ɓauna ne suka cafke Sarkin yayin da yake kan hanyar Kwanar Maharba.
Yan bindigar sun yi harbi yayin da suka ga motar Sarkin Gobir wanda hakan ya jawo suka fasa masa tayoyin mota.
Yadda aka kashe sarkin Gobir
Bayan an kama shi, sarkin Gobir ya bukaci a biya masa kudin fansa ko kuma yan bindigar su kashe shi idan wa'adi ya yi.
Haka kuma aka yi, yan bindigar sun kashe mai martaba Alhaji Isa Bawa a ranar Talata a cikin dajin da suka yi garkuwa da shi.
Rahoton DW Hausa ya nuna cewa wanda suka je jejin domin biyan kudin fansa ne ga yan bindigar suka samu gawar sarkin kwance a kasa.
Halin da ake ciki a Gobir
A halin yanzu masarautar Gobir ta mayar da hankali ne domin ganin ta ƙubutar da dan sarkin sa aka sace su tare.
A ranar Talatar da aka kashe sarkin an kira masu garkuwa da mutane suka ce sarkin yana jin dumi a gafe amma sun ba dansa waya ya yi magana.
Yan bindiga: An fara titi a jejin Sokoto
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Sokoto ta fara ɗaukar matakan kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Tureta ta jihar.
Gwamna Ahmed Aliyu ya amince da gina titin hanya wanda zai ba jami'an tsaro damar zuwa maɓoyar ƴan bindiga domin cimma musu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng