Batun Tsige Akpabio: Kungiyar Tsofaffin Tsagerun Neja Delta Ta Yi Gargadi

Batun Tsige Akpabio: Kungiyar Tsofaffin Tsagerun Neja Delta Ta Yi Gargadi

  • Ƙungiyar tsofaffin tsagerun Neja Delta sun caccaki kiraye-kirayen da wasu ƙungiyoyi ke yi na tsige shugaban majalisar dattawa
  • Tsofaffin tsagerun sun bayyana cewa ko kaɗan ba za su yarda a raba Godswill Akpabio daga muƙamin shugabancin majalisar ba
  • Sun bayyana cewa yunƙurin tsige shi wani sabon rashin adalci ne ga yankin Kudancin Najeriya kuma ba za su amince da hakan ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Ƙungiyar tsofaffin tsagerun Neja Delta ta yi Allah wadai da kiraye-kirayen tsige shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Tsofaffin tsagerun sun bayyana kiraye-kirayen na tsige Akpabio a matsayin wata maƙarƙashiya ga fitattun ƴan siyasan da suka fito daga yankin Kudancin Najeriya.

Tsofaffin tsagerun Neja Delta sun yi gargadi kan tsige Akpabio
Tsofaffin tsagerun Neja Delta sun ce ba za su yarda a tsige Akpabio ba Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Ƙungiyar mai suna 'Niger Delta Ex-Agitators Forum’ ta kuma bayar da shawarar kafa hukumar raya yankin Kudu maso Kudu, daban da hukumar raya yankin Neja Delta, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Shugaban PDP na ƙasa ya fusata, ya yi magana kan yiwuwar ya yi murabus

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙungiyar Alban Paulinus wanda aka fi sani da Janar Skillar ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a birnin Port Harcourt, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

An yi gargaɗi kan shirin tsige Akpabio

Ya bayyana cewa ƙungiyar na sane da ƙoƙarin da wasu mutane ke yi na sauya shugabancin majalisar dattawan, wanda kuma ba za su amince da shi ba.

"Mu ƙungiyar ‘Niger Delta Ex-Agitators Forum’ muna sane da kiraye-kirayen da wasu ƙungiyoyi ke yi na tsige shugaban majalisar dattawa na yanzu, Sanata Godswill Akpabio, wanda ya fito daga Kudancin Najeriya."
"A wajenmu wannan wani sabon rashin adalci ne ga yankin Kudancin ƙasar nan.
"Muna amfani da wannan damar domin mu yi gargaɗin cewa ba za mu lamunci hakan ba, kuma za mu bijirewa duk wani yunƙuri na kawo cikas ga shugabancin Akpabio ta kowace hanya da za mu iya."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi magana kan shirin tsige Ganduje daga mukamin shugabancinta

- Alban Paulinus

Akpabio ya girgiza kan mutuwar Ifeanyi Ubah

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya jagoranci tawagar sanatoci domin yin ta’aziyya ga iyalan marigayi Sanata Ifeanyi Ubah.

Godswill Akpabio ya bayyana cewa ya girgiza matuƙa da rasuwar sanatan domin bai yi tsammanin zai bar duniya a wannan lokacin ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng