Bayan Kwace Jirage, Kamfanin China Ya Karbe Kadarorin Najeriya a Ingila

Bayan Kwace Jirage, Kamfanin China Ya Karbe Kadarorin Najeriya a Ingila

  • Kamfanin kasar China, Zhongshan Fucheng ya sake kwace wasu kadarorin kasar nan da ke kasar waje bayan karbe wasu jirage
  • Lamarin na daga yunkurin kamfanin Zhongshan na karbar Dala Miliyan 70 a matsayin diyyar saba yarjejeniya da gwamnatin Ogun ta yi
  • A wannan jikon, kamfanin ya kwace gidajen saukar bakin Najeriya da ke Liverpool, kuma ta na shirin kwace wasu kadarorin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Liverpool, England - Kamfanin Zhongshan Fucheng Industrial Investment and Co. ya kwace karin kadarorin kasar nan da ke Liverpool a Ingila biyo bayan umarnin kotu.

Kamfanin ya karbe gidajen saukar bakin kasar nan guda biyu, kuma ya na shirin karbar wasu kadarorin a kasashe takwas a Turai da Amurka.

Kara karanta wannan

Tinubu ya dauko muhimmiyar hanyar inganta lantarki, NERC ta ba MTN izini

Bola Tinubu
Kamfanin Zhongshan ya kwace kadarorin Najeriya a Ingila Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa a baya, wata kotun Faransa ta yanke hukuncin da zai ba kamfanin damar karbe jiragen shugaban kasar nan guda uku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kuma yanzu haka kamfanin na shirye shiryen karbe wasu kadarorin a kokarin sa na kwato $70m saboda saba yarjejeniyar 2016 da gwamnatin Ogun ta yi.

Kamfanin China ya fara gwanjon kadarorin Najeriya

Kamfanin Zhongshan Fucheng ya sanya wasu daga cikin kadarorin Najeriya da ya kwace a kasuwa ta manhajar eBay domin samun wasu kudadensa.

Peoples Gazette ta tattaro yadda wata majiya ta bayyana cewa kamfanin zai sa gidajen biyu a kan farashin Dala Miliyan 2.2, domin rage wani kaso na Dala Miliyan 70 dinsa.

Kamfanin ya maka gwamnatin Najeriya kotu bisa zargin saba kwangilar da aka ba shi na gina wurin kasuwanci mara shinge a jihar Ogun.

Kara karanta wannan

PDP v APC: Kotun Koli ta shirya yin hukunci a shari'ar zaben gwamna

Kotu ta amince da kwace kadarorin Najeriya

A wani rahoton kun ji yadda wata kotu a kasar Faransa ta ba kamfanin Zhongshan Fucheng ikon kwace jirage guda uku mallakin gwamnatin Najeriya.

Tuni kamfanin ya kwace jiragen, amma ya saki guda daya domin ba shugaban kasa, Bola Tinubu damar shillawa kasar waje, amma ana shirin kwace wasu kadarorin.

Kamfanin ya yi nasara a kotu inda aka ba shi damar kwace kadarorin Najeriya a kasahen waje har guda takwas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.