Gwamnatin Kano Ta Fadi Abin da Zai Faru kan Zargin Badakalar Kwangilar Magani
- Gwamnatin jihar Kano ta shiga tsaka mai wuya bayan fitaccen mai amfani da kafar sada zumunta, Dan Bello ya zargeta da almundahana
- Dan Bello ya yi zargin kananan hukumomin Kano 44 sun ba wa kamfanin kanin jagoran NNPP, Rabi'u Kwankwaso kwangila
- Baba Halilu Dantiye, kwamishina yada labaran Kano ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta hukunta duk wanda aka samu da hannu a sanar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta bayyana matsayarta kan zargin da ake yi na cewa an ba kamfanin kanin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso kwangila.
Ana zargin kamfanin Musa Garba Kwankwaso na Novomed ya karbi kwangilar samar da magunguna a kan Naira Miliyan 10 ga kowacce karamar hukuma a Kano.
RFI Hausa ta wallafa cewa Baba Halilu Dantiye, kwamishinan yada labarai a Kano za ce tuni aka cika umarnin gwamna Abba Kabir Yusuf na fara binciken lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa gwamna ba zai nuna sanayya a kan duk jami'in da aka kama da aikata ba dai-dai ba kan lamarin da ya dauki hankalin jama'ar kasar nan.
"Gwamnatin Kano ta fara nasara," Dantiye
Kwamishinan yada labaran Kano, Baba Halilu Dantiye ya bayyana cewa tuni hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta fara aikinta a Kano.
Ya ce zuwa yanzu, shugaban hukumar, Barista Muhyi Magaji Rimingado ya fara daukar mataki a kan wadanda ake zargi a cikin badakalar kwangilar, idan ta tabbata.
Kwamishinan ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf ba zai nuna sanayya wajen duba lamarin zargin da ake yiwa wasu daga cikin jami'an gwamnatinsa ba.
Kano: An kama dan uwan Kwankwaso
A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Kano ta tabbatar da kama dan uwan Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da wasu mutane biyar kan zargin badakalar kwangila.
Ana zargin Musa Garba Kwankwaso, mamallakin kamfanin Novomed ya karbi amsar kwangilar Naira Miliyan 10 daga kowacce karamar hukuma ba tare da bin doka ba.
Asali: Legit.ng