Sojojin Sama Sun Hallaka Manyan Kwamandojin 'Yan Ta'adda 5 a Borno, an Jero Sunaye

Sojojin Sama Sun Hallaka Manyan Kwamandojin 'Yan Ta'adda 5 a Borno, an Jero Sunaye

  • Rundunar sojojin saman Najeriya ta bayyana nasarar da dakarunta suka samu kan ƴan ta'adda masu tayar da ƙayar baya a jihar Borno
  • Kakakin rundunar, AVM Edward Gabkwet a cikin wata sanarwa ya ce hare-haren da dakarun rundunar suka kai sun hallaka ƴan ta'adda
  • AVM Gabkwet ya ƙara da cewa an kuma hallaka wasu ƴan ta'adda 35 a yayin hare-haren da aka kai a ranar 15 ga watan Agustan 2024

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun hallaka manyan kwamandojin ƴan ta'adda biyar a jihar Borno.

Sojojin sun hallaka kwamandojin ne tare wasu ƴan ta'adda 35 a wasu hare-haren da jiragen yaƙin rundunar suka kai a yankin Arina, da ke Kudancin Tumbun na jihar Borno.

Kara karanta wannan

Matawalle ya tuna da mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su a Zamfara

Sojojin sama sun hallaka 'yan ta'adda a Borno
Sojojin sama sun hallaka kwamandojin 'yan ta'adda a Borno Hoto: Nigerian Airforce
Asali: Facebook

Kakakin rundunar sojojin saman Najeriya (NAF), AVM Edward Gabkwet, ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 21 ga watan Agusta, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojojin sama suka kashe ƴan ta'adda

A cewar AVM Gabkwet kwamandojin ƴan ta’addan da aka kashe a harin sun haɗa da Munzir Arika, Sani Dilla (Dan Hausawan Jubillaram), Ameer Modu, Dan Fulani Fari Fari, da Bakoura Arina Chiki, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar da haka.

Ya ce an kashe ƴan ta’addan ne a wani farmaki da aka kai musu ta sama a ranar 16 ga watan Agusta.

"Kafin a kai harin, bayanan sirri sun bayyana yadda ƴan ta’addan ke gudun hijira zuwa yankin daga wuraren da ke makwabtaka da shi."
"Sakamakon haka, an ƙaddamar da hare-hare ta sama a wurin, inda aka yi nasarar ritsawa da su wanda hakan ya yi sanadiyyar kawar da ƴan ta'adda da dama tare da lalata maɓoyarsu."

Kara karanta wannan

Yan sanda sun gayyaci shugaban NLC kan zargin ɗaukar nauyin ta'addanci, bayanai sun fito

"Sahihan bayanan sirri sun bayyana cewa an kashe wasu manyan shugabannin ƴan ta’adda biyar ko kuma sun samu munanan raunuka a harin."

- AVM Edward Gabkwet

Sojoji sun hallaka ƴan ta'addan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar sojojin Najeriya sun samu nasara kan ƴan ta'addan Boko Haram a dajin Sambisa na jihar Borno.

Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka ƴan ta'addan Boko Haram mutum shida a maɓoƴarsu da ke cikin dajin tare da ceto mutum 57 daga hannunsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng