Majalisa Ta Gargadi Yan Sanda kan Gayyatar Shugaban NLC, Ta Hango Barazana a Kasa

Majalisa Ta Gargadi Yan Sanda kan Gayyatar Shugaban NLC, Ta Hango Barazana a Kasa

  • Yan majalisa daga jam'iyyun adawa sun caccaki matakin rundunar yan sandan kasar nan na gayyatar shugaban NLC, Joe Ajaero
  • Rundunar ta mika takardar gayyata ga shugaban NLC, Joe Ajaero bisa zargin daukar nauyin ta'addanci yayin zanga-zanga a kasar nan
  • Kakakin kungiyar yan majalisa daga jam'iyyun adawa, Hon. Ikenga Ugochinyere ya ce za a iya jefa kasar nan cikin zanga-zanga

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Yan majalisar wakilai a kasar nan sun bukaci rundunar yan sanda ta janye tuhumar ta'addanci da ta ke yiwa shugaban NLC, Joe Ajaero.

Rundunar ta gayyaci shugaban kungiyar kwadago ta NLC bisa zargin ta'addanci da daukar nauyin zanga-zanga da hada kai wajen tayar da zaune tsaye a lokacin.

Kara karanta wannan

Cikin jam'iyyar APC ya ɗuri ruwa bayan kiran Jonathan ya tsaya takara a zaben 2027

Majalisa
Majalisa ta nemi rundunar yan sanda ta yi watsi da tuhumar shugaban NLC da ta'addanci Hoto: Nigeria Labour Congress HQ/House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa kakakin yan majalisar jam'iyyun adawa, Hon. Ikenga Ugochinyere ya ce tuhumar yan sandan ba ta da makama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Ugochinyere ya kara da cewa kowa na da masaniyar Kwamared Joe Ajaero bai aikata laifin ta'addanci ko kisan kai ba.

Majalisa ta yi gargadin dawowar zanga-zanga

Kakakin yan majalisar kasar nan daga jam'iyyun adawa, Hon. Ikenga Ugochinyere ya ce za a samu martani mara dadi idan yan sanda su ka tsare Joe Ajaero.

Ya ce akwai yiwuwar ma'aikatan kasar nan da sauran jama'a za su kwararo tituna gudanar da zanga-zanga matukar aka kama Kwamred Ajaero, Daily Trust ta wallafa. Dan majalisar ya nemi rundunar yan sanda ta janye zarge-zargen, sannan ta fuskanci magance matsalar tsaro da ya yi kamari a sassan Najeriya.

Zanga-zanga: Yan sanda sun zargi NLC

Kara karanta wannan

Zaben Kano: NNPP ta tanadin katin WAEC da NECO, za a duba takardun karatun yan takara

A baya kun samu labarin cewa rundunar yan sandan kasar nan ta bayyana cewa ta na zargin kungiyar kwadago (NLC) da hannu cikin zanga-zanga.

Babban Sufeton yan sanda, Kayode Egbetokun ne ya bayyana haka, inda ya ce sun gano haka ne bayan kai samame ofishin NLC da ke Abuja a baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.