2027: Bayanai Sun Fito da Manyan Arewa Suka Kira Taro a Sauya Fasalin Siyasa

2027: Bayanai Sun Fito da Manyan Arewa Suka Kira Taro a Sauya Fasalin Siyasa

  • Manyan Arewa sun fara shiri domin kawo sauyi a harkokin siyasar Najeriya da cigaban yankinsu ta fannonin rayuwa mabanbanta
  • Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa za su gudanar da muhimmin taro a jihar Kaduna domin domin daukar mataki a siyasance
  • Taron zai kasance a karkashin kungiyar LND da ta ƙunshi tsofaffin gwamnoni, Sanatoci da mashahuran mutane da suka fito daga Arewa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A yayin taron kungiyar League of Northern Democrats a Abuja, manyan Arewa sun sanar da shirya taro na musamman a jihar Kaduna.

Sanata Ibrahim Shekarau ne fadi haka tare da bayyana cewa taron zai mayar da hankali kan makomar Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Matasa sun kwaci yan fashi a hannun yan sanda, sun cinnawa 1 wuta

Ibrahim Shekarau
Za a yi taron yan Arewa a Kaduna. Hoto: Mallam Ibrahim Shekarau
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa taron na zuwa ne bayan mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya yi kira kan neman hadin kan yan Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a yi taron yan Arewa a Kaduna

Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa za su yi taro a Kaduna domin duba makomar Arewa a kan harkokin tsaro.

Haka zalika Malam Shekarau ya bayyana cewa taron zai mayar da hankali kan siyasar Arewa da kuma tattalin arziki.

Taron yan Arewa zai shafi zaben 2027?

Malam Ibrahim Shekarau ya ce taron ba zai tsaya kan zaben 2027 ba ne kawai, ya ce zai shafi harkokin siyasa ne baki daya.

Sanata Shekarau ya kara da cewa za su samar da tsari ne da zai kunshi manufofin kawo cigaba a Arewa domin tunkarar masu neman kuri'a da tsarin a kodayaushe.

Kara karanta wannan

Shugaban NLC, Ajaero ya yi fatali da gayyatar yan sanda, ya mika bukatunsa

Yadda taron Arewa zai gudana a Kaduna

Jaridar Leadership ta wallafa cewa za a gayyaci manyan yan siyasa, masana da tsofaffin shugabannin Najeriya domin tattaunawa.

Ana sa ran cewa taron zai zamo hanyar magance matsalolin talauci da rashin ilimi da suka yi katutu a Arewa.

Bayani kan rayuwar Ibrahim Shekarau

A wani rahoton, kun ji cewa Ibrahim Shekarau ya yi magana kan abin da ya mallaka kafin ya fito takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2003.

Lokacin da ya yi takara ba shi da N100,000 a cikin asusunsa sannan har ya kusa gama wa'adinsa na biyu bai mallaki gidan kansa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng