Peter Obi Ya Nemi Hakkin 'Yan Kasa, Ya Bukaci Bayanan Sabon Jirgin Tinubu

Peter Obi Ya Nemi Hakkin 'Yan Kasa, Ya Bukaci Bayanan Sabon Jirgin Tinubu

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi ya ce wajibi ne gwamnatin tarayya ta fadi farashin jirgin shugaban kasa
  • A makon nan ne jirgin da fadar shugaban kasa ta sayowa shugaba Bola Tinubu ya iso Najeriya, inda aka tsallake majalisa wajen sayo shi
  • Tuni manyan kasa, ciki har da Peter Obi su ke ganin mutanen Najeriya suna da hakkin samun bayanan farashin da aka sayo jirgin sama

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta yiwa yan kasa bayani game da sabon jirgin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Cikin jam'iyyar APC ya ɗuri ruwa bayan kiran Jonathan ya tsaya takara a zaben 2027

Obi ya mika bukatar ne bayan gwamnati ta yi rufa-rufa wajen sayo jirgin daga wani banki a kasar Jamus, wanda ya iso kasar nan a kwanakin baya.

Peter Obi
Tsohon dan takarar shugaban kasa ya nemi bayanan sabon jirgin Tinubu Hoto: Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Peter Obi na ganin hakkin yan Najeriya ne su san nawa aka dauka daga kudinsu wajen sayo tamgamemen jirgin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon dan takarar ya kara da cewa akwai bukatar a sanar da jama'a shekarun da jirgin ya kwashe ya na aiki gabanin sayo shi.

"Ina tsohon jirgin Tinubu?" - Peter Obi

Peter Obi ya bayyana cewa akwai bukatar fadar shugaban kasa ta sanar da yan Najeriya yadda gwamnati za ta yi da tsohon jirgin da Tinubu ke hawa.

Tsohon dan takarar ya bayyana cewa ba dan kotun kasar Faransa da ta yi tonon silili ba, yan kasar nan ba za su samu tabbacin an sayi jirgin ba.

Kara karanta wannan

Shugaban NLC, Ajaero ya yi fatali da gayyatar yan sanda, ya mika bukatunsa

Ya ce bayyana irin wadannan bayanai da gudanar da gaskiya a gwamnati su ne ginshikin shugabanci na gari da ake bukata, Punch ta wallafa.

An sayawa Tinubu sabon jirgi

A wani labarin kun ji cewa fadar shugaban kasa ta yi gaban kanta wajen sayowa shugaba Bola Ahmed Tinubu sabon jirgin sama ba tare da an bi ta majalisa ba.

Lamarin dai ya dauki hankali ganin cewa fadar shugaban kasar ba ta bayyanawa yan Najeriya farashin sayo jirgin da wani bankin Jamus ya yi gwanjonsa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.