Badakalar Kwangila: An Cafke 'Dan Uwan Kwankwaso, Hadimin Abba da Wasu Mutum 4

Badakalar Kwangila: An Cafke 'Dan Uwan Kwankwaso, Hadimin Abba da Wasu Mutum 4

  • Hukumar yaki da rashawa ta Kano (PCACC) ta cafke dan uwan Sanata Rabiu Kwankwaso da wasu mutane hudu kan zargin ba daidai ba
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya ba da umarnin gudanar da bincike kan zargin an karkatar da kimanin N10bn a kwangilar sayo magunguna
  • Binciken farko na hukumar ne ya ba ta kwarin guiwar kamo Musa Garba Kwankwaso, shugaban karamar hukuma da wasu uku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnatin Abba Kabir Yusuf a jihar Kano ta cafke Musa Garba, wani dan uwan Rabiu Musa Kwankwaso tare da wasu mutane hudu.

Hukumar da ke yaki da rashawa a jihar, PCACC ce ta cafke mutanen kan zarginsu da hannu a wata badakalar kwangila ta samar da magunguna.

Kara karanta wannan

Ba sani ba sabo: Gwamnatin Abba ta dura kan dan uwan Kwankwaso domin bincike

Hukumar CPACC ta cafke dan uwan Kwankwaso da wasu mutum 4
Kano: Hukumar CPACC ta cafke mutum 5 ciki har da dan uwan Kwankwaso. Hoto: @MuhuyiMagaji
Asali: Facebook

Gwamnati ta cafke dan uwan Kwankwaso

Arise News ta rahoto PCACC ta cafke mutane biyar da suka hada da dan uwan Kwankwaso, da kuma babban sakatare a ma'aikatar kananan hukumomi, Mohammed Kabawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran da aka kama sun hada da shugaban kungiyar kananan hukumomi ALGON na jihar, Abdullahi Bashir wanda kuma shi ne shugaban karamar hukumar Tarauni.

Hakazalika, hukumar yaki da rashawar ta cafke shugaban kamfanin magunguna na Novomed, Musa Kwankwaso, dan uwa ga jagoran NNPP na kasa.

Dalilin kama dan uwan Kwankwaso

An zargi wadanda aka kama da hada baki wajen ba kamfanin Novomed kwangilar samar da magunguna ga kananan hukumomin jihar ba tare da bin dokar ba da kwangila ba.

Binciken farko ya nuna cewa kowace daga cikin kananan hukumomin 38 sun biya Novomed N9.150m domin siyan magunguna amma har yanzu ba a kawo musu magunguna ba.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Gwamnatin Kaduna ta bullo da matakin ceton mazauna kananan hukumomi 7

"Binciken ya kuma nuna cewa dukkanin wadanda ake zargin suna bayar da hadin kai ga tawagar binciken hukumar."

- Inji wata majiya, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

PCACC ta yi magana kan kamen

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Kabiru Kabiru ya tabbatar da kamen, inda ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike.

Mista Kabiru ya ce hukumar na kokarin bankado yadda aka gudanar da zambar sayo magungunan tare da gurfanar da wadanda ke da hannu a gaban kuliya.

Ya kuma tabbatar da cewa wadanda ake zargin suna hannun hukumar a lokacin da aka gabatar da rahoton farko.

Gwamnati ta yi wa Dan Bello martani

Tun da fari mun ruwaito cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya umarci hukumar PCACC da ta gudanar da bincike kan badakalar kimanin N10bn ta sayo magunguna daga Novomed.

Gwamna Abba Yusuf, ya musanta m,asaniya kan kwangilar da aka ba kamfani Novamed mallakin dan uwan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, kamar yadda binciken Dan Bello ya nuna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.