Jerin Ƙasashe 5 da Suka Fi Sauki da Arahar Rayuwa a Nahiyar Afirka a 2024
Hauhawar farashin kayayyaki biyo bayan cutar COVID-19 da aka yi fama da ita a 2020 ya jefa ƙasashen duniya cikin wahala da tsadar rayuwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Kasashen nahiyar Afirka ba su tsira daga tasirin hauhawar farashin kayayyakin ba, wanda ya shafi kudaden shiga na galibin ma'aikata da sauran al'umma.
A baya-bayan nan dai kasashe irinsu Kenya da Najeriya sun fuskanci zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa, inda 'yan kasar suka bukaci gwamnatocinsu da su dauki mataki.
Kasashen Afrika da ake samun saukin rayuwa
Duk da haka akwai ƙasashen Afirka da ke rayuwa mai sauki idan aka kwatanta da wasu ƙasashen, kamar yadda Vanguard ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wannan babin, Legit Hausa ta tattaro muku ƙasashe biyar a Afirka masu saukin rayuwa a wannan shekarar da muke ciki 2024.
1. Libya
Duk da rikicin da take fama da shi, ƙasar Libya na sahun gaba a jerin kasashen Afirka da ke da sauƙin rayuwa.
Dogaron ƙasar da arzikin man fetur da kuma kokarin daidaita kowane ɓangare na tattalin arziki na taka muhimmiyar rawa wajen sauke farashi daidai gwargwado.
Alal misali, an yi ƙiyasin cewa idan aka cire kuɗin haya, $1,327.50 (6,388.30 LYD) za ta riƙe magidanci mai iyalin mutum huɗu a wata.
Haka nan kuma gwauro wanda ke rayuwa shi kaɗai zai kashe abin da bai wuce $374.80 (1,803.50 LYD) a wata idan ba ya biyan kuɗin haya a ƙasar Libya.
A taƙaice dai Libya ta fi Najeriya sauƙi da arahar rayuwa da kaso 33.3% a matsakaicin kiyasin da aka yi, rahoton Bussines Insider.
2. Masar
Kasar Masar, da aka santa da dimbin tarihi da al'adu, tana da arahar rayuwa da sauƙin tashin farashi idan aka kwatanta da wasu ƙasashe a Afirka.
Hanyoyin tara kuɗaɗen shigar ƙasar kamar noma, wuraren yawon buɗe ido da masana'antu suna ba da gudummuwa wajen rage yawan kashe ƙuɗi.
Alal misali, iyali mai mutum huɗu za su rayu da $1,159.50 (56,927.30 EGP) a wata ba tare da biyan haya ba, yayin da gwauro kuma zai ci $327.70 (16,088.10 EGP) a wata.
A matsakaicin ƙiyasin da aka yi, tsadar rayuwa a Masar ta yi kasa da kashi 32.4% idan aka kwatanta da Najeriya.
3. Tanzaniya
Ƙasar Tanzaniya ta shahara da arahar rayuwa musamman saboda ƙarfin da take da shi a ɓangaren noma, yawon buɗe ido, da sauran albarkatun ƙasa da Allah ya ba ta.
Idan aka jingine kuɗin haya, Iyali mai mutane hudu yawanci suna kashe $1,503.60 (4,064,149.20 TSh) a wata yayin da mutum ɗaya ke buƙatar $436.70 (1,180,447.40 TSh).
Gaba ɗaya dai rayuwa a Tanzaniya tana da araha matuƙa da kashi 11.5% fiye da a Najeriya.
4. Madagascar
Duk da kalubalen tattalin arzikin da ƙasar ke fama da su, yawan albarkatun kasa da ayyukan noma na taimakawa wajen samun saukin rayuwa a Madagascar.
Idan muka ɗauki sikelin iyali mai mutum hudu, an yi ƙiyasin $1,383.60 (6,301,103.90 Ar) za ta iya riƙe su a wata yayin da mutum ɗaya ke bukatar aƙalla $401.80 (1,829,979.70Ar).
A bisa matsakaicin ƙiyasi, Madagascar ta fi Najeriya sauki da arahar rayuwa da kaso 22.8%.
5. Tunisiya
Tunisiya da ke Arewacin Afirka ƙasa ce da ta dogara da abubuwa daban-daban na tattalin arziki, kuma tana da matsakaicin farashin kayayyaki, da darajar kuɗi.
A ƙasar an kiyasta cewa $1,602.60 (4,930.30 DT) za ta riƙe gida mai mutum huɗu, gwauro kuma shi kaɗai zai yi matsakaiciyar rayuwa da $454.60 (1,398.60 DT) a wata.
Ƙasar Tunisiya ta ɗara Najeriya arhar rayuwa da kaso 7.1% kamar yadda alƙaluman kididdga suka bayyana.
Farashin gas ya sauka a Najeriya
A wani rahoton kun ji cewa hukumar kididdiga ta Najeriya (NBS) ta fitar da rahoton farashin gas din girki da aka fi sani da LPG na watan Yulin 2024.
Rahoton hukumar ya nuna an samu karyewar farashin gas din a watan Yuli da 14.23% idan aka kwatanta shi da na Yuni.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng