Gwamna Zulum Ya Cika Aiki, Tallafin Shugaba Tinubu Ya Isa Hannun Magidanta 10,000
- Kashin karshe na tallafin tireloli 20 da gwamnatin tarayya ta tura Borno ya isa hannun mutane a karamar hukumar Mafa
- Gwamna Babagana Umaru Zulum ya rabawa magidanta 10,000 tallafin hatsi a ranar Talata, 20 ga watan Agusta, 2024
- Zulum ya kuma raba tallafin tsabar kudi N150m ga mata domin su kama sana'a, sannan ya miƙa godiya ga Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum ya rabawa magidanta 10,000 tallafin hatsin da gwamnatin tarayya ta turo jihar.
Gwamma Zulum ya kuma ciro N150m daga asusun gwamnatin Borno, ya rabawa mata domin yabawa kokarin gwamnatin tarayya duba da halin da ake ciki.
The Nation ta tattaro cewa Farfesa Zulum ya rabawa magidanta wannan tallafi ne a ƙaramar hukumar Mafa da je jihar Borno.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi a wajen taron raba tallafin a garin Mafa a ranar Talata, Zulum ya ce hatsin shi ne kashin karshe na tireloli 20 da gwamnatin tarayya ta turo.
Bola Tinubu ya rabawa jihohi tirela 20
A makonnin baya gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za ta ba kowace jiha da Abuja tallafin tirela 20 na shinkafa da kayan hatsi domin a rabawa talakawa.
Ministan yaɗa labarai, Muhammed Idris, ya ce an ɗauki wannan matakin ne domin sauke farashin abinci da kuma ragewa al'umma raɗaɗin ƙuncin rayuwa.
Gwamna Zulum ya yabawa gwamnatin Tinubu
Gwamna Zulum ya yabawa gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa tallafin da take bai wa jama'a domin rage raɗaɗi, NTA News ta rahoto.
Kazalika gwamnan ya roƙi ƴan Najeriya da su ba Gwamnatin Bola Tinubu goyon bayan da take buƙata kuma su fahimci tsare-tsaren da ta ɗauko domin saita ƙasar nan.
Hakan a cewarsa, zai ba gwamnati a dukkan matakai damar aiwatar da karin tsare-tsare da manufofin da za su rage wahalhalun da jama’a ke ciki.
Gwamna ya tallafawa waɗanda suka yi haɗari
A wani rahoton kun ji Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu ya ware tallafin N30m ga waɗanda hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a kauyen Dundaye.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta bai wa iyalan mutum biyar da suka rasu a haɗarin N15m yayin da waɗanda suka tsira kuma za a ba su N15m.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng