Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce, Bayanai Sun Fito

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce, Bayanai Sun Fito

  • Tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Anambra ya fadi matacce a ranar Litinin 19 ga watan Agustan 2024
  • An ruwaito cewa tsohon dan majalisar ya yanke jiki ya fadi bayan gama motsa jiki a filin wasa na Alex Ekwueme da ke Awka
  • An ce an dauki gawar dan siyasar an kai ta cibiyar kiwon lafiya ta Apex da ke birnin Awka, nan aka tabbatar da mutuwarsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - An shiga jimami yayin da Rt. Hon. Hardford Oseke, tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Anambra ya yanke jiki ya fadi matacce.

An ce labarin ya faru ne a ranar Litinin lokacin da tsohon dan majalisar ya yanke jiki ya fadi a lokacin da ya gama motsa jiki a filin wasa na Alex Ekwueme da ke Awka.

Kara karanta wannan

Daga karin kumallo, uwa da ƴaƴanta 3 sun rasu a wani yanayi mai ban tausayi

Tsohon mataimakin kakakin majalisar Anambra ya rigamu gidan gaskiya
An sanar da mutuwar tsohon mataimakin kakakin majalisar Anambra, Hardford Oseke. Hoto: Ike Orumba
Asali: Facebook

Tsohon mataimakin kakakin majalisa ya mutu

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa an yi duk wani kokari na ganin an farfado da Hon. Hardford bayan faduwarsa amma hakan ya ci tura.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce an dauki gawarsa an kai ta cibiyar kiwon lafiya ta Apex da ke Awka bayan da aka tabbatar da mutuwarsa a ranar 19 ga watan Agustan 2024.

Iyalai, 'yan uwa da abokan arzikin dan siyasar sun shiga cikin tashin hankali da mamaki bayan samun labarin mutuwarsa, kasancewar ya fita gida cikin koshin lafiya.

Takaitaccen bayani kan Hon. Hardford Oseke

Wanda aka haifa a shekarar 1960, Hon. Hardford ya fito ne daga garin Umuawulu da ke karamar hukumar Awka ta Kudu da jihar Anambra.

An ce kusan siyasarsa ta jingina ne da jam'iyyar APGA, inda ya nemi takarar dan majalisar dokoki a lokacin mulkin Peter Obi, inji rahoton New Telegraph.

Kara karanta wannan

Murna za ta koma ciki? Ambaliya ta fara barazana ga wadatar abinci

Hon. Hardford ya rike mukamin shugaban masu rinjaye na majalisar kafin daga bisani ya samu damar zama mataimakin kakakin majalisar.

Dan majalisar wakilai ya mutu a Jigawa

A wani labarin a baya, mun ruwaito cewa dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabun Garki da Babura a jihar Jigawa, Isa Dogonyaro ya rasu.

An ce dan majalisar ya rasu ne a ranar Jumu'ah, 10 ga watan Mayu a Abuja bayan gajeruwar jinya da ya yi kuma an yi masa sutura bisa tsarin addini.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.