Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama kan Shari'ar Tsige Mataimakin Gwamnan PDP

Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama kan Shari'ar Tsige Mataimakin Gwamnan PDP

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta raba gardama kan taƙaddamar da ake yi dangane da tsige mataimakin gwamnan jihar Edo
  • Kotun ta tabbatar da hukuncin babbar kotun tarayya wanda ya soke tsige Philip Shaibu daga muƙamin da yake kai
  • An yi watsi da ƙarar da majalisar dokokin Edo ta shigar tana buƙatar a tabbatar da tsige Kwamred Philip Shaibu da ta yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Kotun ɗaukaka kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta yanke hukunci kan taƙaddamar kujerar mataimakin gwamnan Edo.

Kotun ɗaukaka ƙarar a ranar Talata, ta tabbatar da hukuncin da kotu ta yi na mayar da Philip Shaibu a matsayin mataimakin gwamnan jihar Edo.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakin tabbatar da ƴancin ƙananan hukumomi a Najeriya

Kotun daukaka kara ta tabbatar da kujerar Philip Shaibu
Kotun daukaka kara ta tabbatar da Philip Shaibu a matsayin mataimakin gwamnan Edo Hoto: @HonPhilipShaibu
Asali: Twitter

Kotu ta tabbatar da kujerar Philip Shaibu

Kotun ɗaukaka ƙarar a lokacin da take yanke hukunci, ta yi watsi da ƙarar da majalisar dokokin jihar Edo ta shigar a gabanta, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar dokokin ta jihar Edo dai ta buƙaci kotun da ta tabbatar da tsige mataimakin gwamnan da ta yi.

An tsige Philip Shaibu ne a ranar 8 ga watan Afrilu, 2024, bayan amincewa da rahoton kwamitin mutum bakwai da babban alƙalin jihar Edo mai shari’a Daniel Okungbowa ya kafa domin bincikar zarge-zargen da ake yi masa.

Kotu ta soke tsige Philip Shaibu

Mai shari’a James Omotosho na wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja a ranar 17 ga watan Yuli, ya yi watsi da tsige Philip Shaibu a matsayin mataimakin gwamnan.

Alƙalin ya kuma bayar da umarnin mayar da shi kan muƙaminsa ba tare da ɓata lokaci ba.

Kara karanta wannan

Manyan ƴan siyasa, tsofaffin hadiman Ganduje sun kafa kungiya da manufa 1 a Kano

Kotun ta yi gargaɗin cewa duk wanda ya bayyana kansa a matsayin mataimakin gwamnan jihar idan dai ba Philip Shaibu ba ne zai fuskanci hukuncin shari'a.

Kotun ta kuma yi watsi da naɗin Omobayo Godwin a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar, wanda ya maye gurbin Philip Shaibu.

Philip Shaibu ya caccaki Gwamna Obaseki

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu, ya ƙaryata batun cewa Gwamna Godwin Obaseki ne ya sa aka san shi a siyasance.

Philip Shaibu ya bayyana cewa shi ne ya yiwa gwamnan rana a siyasance domin nemansa aka yi ya zo ya yi masa mataimakin gwamna saboda ya taimake shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng