Shugaban NLC, Ajaero Ya Yi Fatali da Gayyatar Yan Sanda, Ya Mika Bukatunsa
- Bayan NLC ta amince da mutunta gayyatar da jami'an tsaro su ka yiwa shugabanta, Joe Ajaero ya ce ya fasa
- Rundunar yan sandan kasar nan ta gayyaci Joe Ajaero domin ya amsa tambayoyi kan zargn daukar nauyin ta'addanci
- Lauyan NLC kuma mai fafutuka kare hakkin dan Adam, Femi Falana SAN ya kawo uzurin kin zuwa gaban 'yan sandan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Kungiyar kwadago ta bayyana cewa shugabanta, Kwamred Joe Ajaero ba zai iya mutunta gayyatar da ta yi masa ba bisa wasu dalilai.
Lauyan NLC, kuma fitaccen mai kare hakkin dan Adam, Femi Falana SAN ne ya bayyana haka bayan taro da kusoshin kungiyar a kan gayyatar zargin.
Femi Falana ya tsayawa shugaban NLC
Jaridar The Cable ta tattaro cewa Femi Falana ya bukaci rundunar yan sandan ta jero dukkanin zarge-zargen da ta ke yiwa shugaban kwadagon.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar yan sanda ta ce ta na zargin Joe Ajaero da hada baki da kuma daukar nauyin ta'addanci a lokacin zanga-zangar adawa da gwamnatin Bola Tinubu.
Ajaero ya sa ranar amsa gayyatar yan sanda
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa shugaban NLC, Joe Ajaero ta bakin lauyansa, Femi Falana ya ce ya na da abin da zai yi a ranar 20 Agusta, 2024.
Wannan dalili ya sa ba zai iya mutunta kiran da rundunar yan sandan kasar nan ta yi masa kan zargin ta'addanci ba, amma zai amsa gayyatar a ranar 29 Agusta, 2024.
Femi Falana ya kuma bukaci karin bayani kan zargin ta'addanci da hada baki wajen daukar nauyinsa da rundunar ke yiwa Ajaero kamar yadda doka ta tanada.
Yan sanda sun gayyaci shugaban NLC, Ajaero
A baya kun ji cewa rundunar 'yan sandan kasar nan ta mika takardar gayyata ga shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC) domin amsa tambayoyi.
Rundunar ta ce ta na zargin Kwamred Ajaero da hannu cikin daukar nauyin ta'addanci, saboda haka ta nemi ya bayyana a gabanta da safiyar Talata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng