Gwamnatin Sokoto Ta Lalubo Hanyar Kawo Karshen 'Yan Bindiga

Gwamnatin Sokoto Ta Lalubo Hanyar Kawo Karshen 'Yan Bindiga

  • Gwamnatin jihar Sokoto ta fara ɗaukar matakan kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Tureta ta jihar
  • Gwamna Ahmed Aliyu ya amince da gina titin hanya wanda zai ba jami'an tsaro damar zuwa maɓoyar ƴan bindiga
  • Gwamnan wanda ya ce ya damu matuƙa kan ayyukan ƴan bindiga, ya buƙaci jama'a su ci gaba da yiwa gwamnati addu'a

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta ɗauki matakin kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Tureta ta jihar.

Gwamnatin ta amince da gina titin hanyar Tureta-Gidan Kare domin samun damar zuwa inda ƴan bindiga ke ɓoyewa.

Gwamnan Sokoto ya amince da gina hanya
Gwamnan Sokoto na rangadin kananan hukumomi Hoto: @AhmedAliyuskt
Asali: Facebook

Gwamnan jihar, Ahmed Aliyu ne ya bayyana hakan yayin ziyarar da ya kai ƙaramar hukumar Tureta a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya ciri tuta, zai fara biyan ma'aikata sabon mafi karancin albashi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya je ƙaramar hukumar ne a wani rangadin da ya ke yi na ƙananan hukumomi 23 na jihar, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Gwamnan Sokoto na son kawo ƙarshen ƴan bindiga

A cewarsa, idan aka kammala hanyar za ta sanya jami’an tsaro su samu sauƙin shiga dazuzzukan da ke zama maɓoyar ƴan bindiga a yankin.

"A matsayinmu na gwamnati, mun himmatu wajen samar da duk abin da ya dace domin tabbatar da cewa ƙauyukanmu sun zauna lafiya tare tsira daga duk wani ƙalubale na tsaro."
"Ina ba ku tabbacin cewa za mu kashe duk abin da muka mallaka domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummarmu."
"Mun damu matuƙa da munanan ayyukan da ƴan bindiga ke yi a jiharmu, kuma muna ƙara ɗaukar matakan kawo ƙarshen wannan matsala Insha Allahu."

- Gwamna Ahmed Aliyu

Kara karanta wannan

Mutum 2 ƴan gida sun mutu a wani mummunan ibtila'i da ya rutsa da su a Arewa

Gwamnan Ahmed Aliyu ya kuma yi kiran da a ci gaba da yi wa gwamnati addu'a da nuna mata goyon bayan domin cimma ƙudirin da ta sanya a gaba.

Gwamnatin Sokoto ta karya farashin shinkafa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Sokoto ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta ƙara azama a ƙoƙarinta na karya farashin kayayyakin abinci na yau da kullum.

Gwamnatin ta fara shirin sayo tirelolin shinkafa 300 tare da sayarwa mutanen Sokoto a farashi mai rahusa saboda tsadar rayuwar da ake fama da ita.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng