Miyagu na Yi wa Jami'an Tsaro Dauki Dai dai, An Kona Wani har Gida a Katsina

Miyagu na Yi wa Jami'an Tsaro Dauki Dai dai, An Kona Wani har Gida a Katsina

  • Rashin tsaro na sauya salo a Katsina, miyagu sun fara kai hari har gidajen jami'in sa kai, tare da yi masa kisan gilla
  • Miyagun sun kai harin rashin imani gidan Aliyu Yahaya da ke cikin kungiyar mafarauta a jihar, inda su ka kashe shi
  • Haka kuma sun bankawa gawarsa wuta, daga bisani su ka sace matarsa , dansa da makwabta ba tare da an hana su ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina - Wasu miyagu sun kai harin rashin tausayi kan wani dan kungiyar mafarauta a Katsina, inda su ka kashe shi tare da kone gawarsa.

Kara karanta wannan

Daga karin kumallo, uwa da ƴaƴanta 3 sun rasu a wani yanayi mai ban tausayi

'Yan ta'addan sun kuma yi awon gaba da iyalan marigayin mai suna Aliyu Yahaya, mazaunin Magamar Jibia, a karamar hukumar Jibia da ke Katsina.

Katsina
Miyagu sun kashe jami'in sa kai a Katsina Hoto: Katsina State Government
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa baya ga iyalan marigayi Aliyu, yan ta'addan sun yi garkuwa da makwabtansa guda uku a ranar Talata, 13 Agusta, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Salisu Yahaya, kanin marigayin ya ce duk da yayansa ya yi kokarin tirjewa, amma sun fi karfinsa, sannan su ka kashe shi, tare da kona shi a dakinsa.

Yan sanda sun shiga farautar miyagu

Rundunar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da harin miyagu da ya yi sanadiyyar rasuwar mafarauci a jihar, Aliyu Yahaya mai shekaru 31 a gidansa.

ASP Abubakar Sadiq, shi ne jami'in hulda da jama'a na jihar, ya kuma tabbatar da cewa yanzu haka sun shiga farautar miyagun da zummar ceto wadanda aka sace.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun matsawa mutane, sun farmaki kananan hukumomin Katsina

Jama'ar garin sun fusata da yadda babu jami'an tsaro a yankin, inda su ka nemi yan sanda su rika ceto wadanda aka sace domin saukakawa iyalansu radadin.

Miyagu sun kai hari Katsina

A wani labarin, kun ji cewa miyagu sun takurawa mazauna Katsina, inda su ka kai hari kananan hukumomi guda biyu, tare da sace matan aure da kananan yara.

'Yan ta'addan sun kai hari karamar hukumar Musawa da Kankara, kuma su ka yi nasarar awon gaban da mutanen da ba a tabbatar da yawansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.