Ajaero: NLC Ta Ja Daga, Ta Fadi Tsattsauran Mataki idan aka Kama Shugabanta

Ajaero: NLC Ta Ja Daga, Ta Fadi Tsattsauran Mataki idan aka Kama Shugabanta

  • Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta bukaci ma'aikata su kwana cikin shirin rufe dukkanin sassan tattalin arzikin kasa
  • Wannan na zuwa bayan jami'an tsaro sun mika goron gayyata ga shugaban kungiyar, Joe Ajaero domin amsa tambayoyi
  • A sanarwar da ta fitar, kungiyar ta ta ce idan aka tsare Kwamred Ajaero, ba za su tsaya wasa wajen daukar mataki ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Kungiyar kwadago ta kasa (NLC), ta sanar da ya'yan kungiyar da sauran ma'aikatan kasar nan su kwana da shirin daukar mataki kan gwamnati.

Bayanin na zuwa bayan gayyatar da jami'an tsaro su ka yi wa shugaban kungiyar, Joe Ajaero bisa zargin daukar nauyin ta'addanci da daukar nauyin zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Shugaban NLC, Ajaero ya yi fatali da gayyatar yan sanda, ya mika bukatunsa

Kungiya
Shugaban NLC zai amsa gayyatar yan sanda Hoto: Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Facebook

A sanarwar bayan taron gaggawa da kungiyar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce ta nemi a kara mata lokaci domin ganawa a da lauyoyi kafin kwamred Ajaero ya amsa gayyatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta ce kiran shugabanta, kira ne ga daukacin ma'aikatan kasar nan, saboda haka su kwana cikin shiri.

Shugaban NLC zai amsa gayyatar jami'an tsaro

NLC ta ce shugabanta, Kwamred Joe Ajaero zai amsa gayyatar da jami'an tsaro su ka yi masa bisa zargin daukar nauyin ta'addanci, Solace Base ta wallafa.

Mataimakin shugaban NLC, Kabiru Ado Sani ya bayyana cewa NLC halastacciyar kungiya ce, saboda haka ba sa fargabar kai kansu gaban jami'an tsaro idan akwai bukatar hakan.

Uwar kungiyar NLC ta ce za ta ci gaba da bibiyar lamarin, kuma da zarar an dauki wani mataki za a sanar da jihohi, domin su sanar da jama'arsu a aiwatar da matsayar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya tono illar tallafin lafiya, ya gindayawa kungiyoyi sharadin taimako

Jami'an tsaro sun gayyaci shugaban NLC

A baya, mun ruwaito cewa wasu jami'an tsaro sun nemi shugaban kungiyar kwadago na kasa (NLC), Joe Ajaero da ya bayyana gabanta ya amsa tambayoyi.

Yan sandan na zargin NLC na da hannu wajen daukar nauyin zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Bola Tinubu da aka shafe kwanaki 10 ana yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.