N70,000: NLC Ta Fadi Lokacin da Za a Kammala Shirin Fara Biyan Sabon Albashi
- Mataimakin shugaban kungiyar kwadago na kasa ya magantu kan yadda aka samun jinkirin biyan mafi ƙarancin albashi
- Farfesa Theophilus Ndubuaku ya ce akwai abubuwa da dama wanda dole sai an kammala su kafin a fara biyan sabon albashi
- Sai dai duk da haka ya bayyana cewa ana sa ran a karshen watan Agusta za a kammala dukkan ayyukan da suka kawo tsaikon
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar kwadago ta yi bayani kan halin da ake ciki a kan soma biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Yan kwadago sun ce an samu jinkiri ne saboda wasu abubuwa kamar tattara bayanai da suka zama dole a warwaresu.
Jaridar Punch ta wallafa cewa mataimakin shugaban kwadago na kasa, Farfesa Theophilus Ndubuaku ne ya yi bayanin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin samun jinkirin ƙarin albashi
NLC ta bayyana cewa ayyukan tattara bayanan ma'aikata da sauransu na cikin abubuwan da suka kawo jinkirin fara biyan sabon albashi.
Farfesa Theophilus Ndubuaku ya ce akwai kwamitin da aka tanada domin yin wannan aikin kuma ba barci suke ba tun da suka fara aikin.
Yaushe za a kammala aikin?
Legit ta ruwaito cewa Farfesa Theophilus Ndubuaku ya bayyana cewa suna kyautata zaton cewa nan da ƙarshen watan Agusta ake saka ran kammala aikin.
Ana sa ran cewa da zarar an kammala aikin za a iya fara biyan ma'aikata mafi ƙarancin albashi na N70,000.
NLC ta yi kira ga yan Najeriya
A karkashin ƙoƙarin da ake yi, kungiyar kwadago ta ce ya kamata yan Najeriya su san jinkirin ba wai da gangan ake yinsa ba.
Saboda haka ta bukaci yan Najeriya da su kara hakuri da gwamnatin tarayya har zuwa lokacin da za a kammala aikin a fara biyan albashin.
Gwamnan Adamawa zai biya albashin N70,000
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Adamawa za ta fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 da gwamnatin tarayya ta amince da shi.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya amince a fara biyan ma'aikatan jihar sabon mafi ƙarancin albashin daga watan Agustan 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng