UBEC: Kano da Wasu Jihohi 3 a Arewa Sun Yi Asarar Tallafin Sama da N4bn a 2023
- Kano, Kaduna da wasu jihohin Arewa maso Yamma sun gaza cika sharuɗɗan cin gajiyar tallafin ilimin yara N4.7bn daga hukumar ilimi
- Alkaluma sun nuna waɗannan jihohin suna a sahun gaba wajen yawan kananan yaran da ba su zuwa makarantar boko a Najeriya
- Hukumar UBEC dai tana ware tallafin ne domin magance yawan ƙananan yaran da ba su zuwa makaranta a ƙasar nan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Duk da yawan yara masu gararamba a kan tituna, jihohi huɗu daga Arewa maso Yamma sun gaza cika sharuɗɗan da ya dace domin karɓo tallafin ilimin yara N4.7bn daga UBEC.
Jihohin sun haɗa da Kano, Katsina, Kaduna da kuma Kebbi, waɗanda su na sahun gaba a jihohi masu yawan yaran da ba su zuwa makaranta a Najeriya.
A wasu alƙaluma da hukumar ilimin bai ɗaya ta ƙasa (UBEC) ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta nuna cewa jihohin sun gaza cin gajiyar tallafin ilimin a 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kuɗin da jihohin suka gaza samu daga UBEC
Bayanai na baya-bayan nan da UBEC ta wallafa sun nuna cewa Kaduna ta gaza karɓo N1.39bn, Kano N581.5m, Katsina N1.39bn da Kebbi N1.39bn.
Hakan dai ta faru ne duk da faɗi tashin hukumar UBEC na ganin ta magance yawaitar kananan yara da ke gararamba a gari ba tare da zuwa makaranta ba.
Kididdiga ta nuna kashi 29% na ƙananan yaran da suka isa fara zuwa makaranta suna gararamba a Kaduna, adadin ya kai 35% a Kano, 38% a Katsina da 45.% a Kebbi.
Arewa na fama da rashin ilimi
Har ila yau an tattaro cewa waɗannan jihohi huɗu suna da ƙananan yara miliyan 4.8 waɗanda ba su zuwa makaranta.
Jihar Kano kaɗai tana da yara miliyan 1.890 da ke yawo a gari, Katsina na da miliyan 1.4, Kebbi na da miliyan 1.060 yayin da Ƙaduna ke da 660,000.
Bayanai sun nuna wasu sharuɗɗar samar da ilimin boko ga yara jihohin za su cika domin karɓar tallafin ilimin daga hukumar UBEC, amma suka gaza hakan a 2023.
Hukumar UBEC tana ware waɗannan makudan kuɗin ne domin magance yawaitar yaran da ba su zuwa makaranta.
Sakamakon jarabawar WAEC ya fito
A wani rahoton kuma hukumar shirya jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC) ta fitar da sakamakon jarrabawar kammala sakandare (WASSCE) ta 2024.
Kimanin dalibai 1,814,344 ne daga makarantun sakandare 22,229 a fadin kasar nan ne aka ce sun zana jarrabawar WASSCE 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng