Gwamnati Ta Yi Bayani kan Umarnin Tinubu na Biyan ‘Kudin Tallafin Mai’
- Gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan maganar da Bola Tinubu ya yi ga kamfanin NNPCL kan cigaba da biyan kudin tallafin man fetur
- Shugaban harkar tattara kudi na kamfanin NNPCL, Alhaji Umar Ajiya ne ya yi bayanin ga yan Najeriya bayan al'umma sun shiga ruɗani
- A jiya Litinin ne aka shiga ruɗani bayan an samu bayanai kan cewa shugaban kasa ya yi umarni da a dawo da tallafin man fetur
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan maganar shugaba Bola Tinubu ta maido tallafin mai fetur.
Shugaban tattara kudi a kamfanin NNPCL, Alhaji Umar Ajiya ne ya bayyana abin da gwamnati take nufi.
Jaridar the Cable ta wallafa cewa Alhaji Umar Ajiya ya yi bayanin ne a ranar Litinin a birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPCL: 'Babu maganar dawo da tallafin mai'
Alhaji Umar Ajiya ya bayyana cewa ba maganar dawo da tallafin mai da ake raɗe radin gwamnati ta yi.
Ya kuma tabbatar da cewa tun da aka cire tallafin gwamnatin tarayya ba ta sake biyan wani kudin tallafi ko kobo ba.
Maganar Tinubu ta maido tallafin mai
Haka zalika Alhaji Umar Ajiya ya ce abin da yake faruwa shi ne suna sayen man fetur daga ƙasashen waje a farashi mai tsada.
Idan kuma suka kawo shi Najeriya sai su sayar da shi a rabin farashin kasuwa domin kaucewa tsadarsa a Najeriya.
Bambancin rage kudi da tallafin mai
Daily Trust ta wallafa cewa Alhaji Umar Ajiya ya bayyana cewa akwai bambanci tsakanin biyan tallafin man fetur da kuma rage farashinsa zuwa rabi.
Ya kara da cewa bambancin shi ne rage farashin yana faruwa ne tsakanin gwamnatin tarayya da kamfanin NNPCL amma tallafi kuma yana faruwa tsakanin gwamnati da yan kasuwa ne.
Atiku ya yi magana kan tallafin mai
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan maganar tallafin man fetur.
Atiku Abubakar ya buƙaci gwamnatin Bola Tinubu ta fito ta yi bayani ga yan Najeriya kan hakikanin abin da yake faruwa kan tallafin man fetur da zance ya gaza fita fili.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng