IPMAN Ta Dora Alhakin Karancin Fetur kan NNPCL, Ta Zargi Kamfanin da Kawo Matsala

IPMAN Ta Dora Alhakin Karancin Fetur kan NNPCL, Ta Zargi Kamfanin da Kawo Matsala

  • Kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN), ta zargi kamfanin NNPCL da jawo karancin man fetur a fadin Najeriya
  • IPMAN ta zargi NNPCL da hana su fetur din da za su kai gidajen mai da 'ya'yan kungiyar sama da 3000 su ka mallaka a kasar nan
  • Shugaban IPMAN da ke wurin sauke fetur na Ore, Shina Amoo ya ce NNPCL ya fi shekara uku bai ba su fetur din da ake bukata ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Kungiyar dillalan man fetur (IPMAN) ta bayyanawa 'yan Najeriya cewa kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ne ke jawo karancin fetur.

Kara karanta wannan

Maido tallafin mai: Kamar Atiku, an zargi NNPCL da rashin fito da bayanai filla filla

Kungiyar ta bayyana cewa ta na da 'yan kasuwa akalla 3000 da su mallaki gidajen mai a fadin kasar nan, amma NNPCL ya hana su fetur da za su kai gidajen.

IPMAN
PMAN ta zargi NNPCL da jawo karancin fetur Hoto: Benson Ibeabuchi
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban IPMAN a Ore, Shina Amoo ya ce duk da kamfanin NNPCL ne kadai ke shigo da fetur, an fi shekara uku ba a ba su isasshen fetur ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"NNPCL ba ya ba mu fetur," IPMAN

Channels Television ta wallafa cewa kungiyar IPMAN ta zargi kamfanin NNPCL da kin ba su fetur da zai wadaci bukatar da yan kasar nan ke da shi.

Shugaban IPMAN a Ore, Shina Amoo ya zargi IPMAN da ware 'yan kungiyarta da gan-gan, inda ta ke ba wa sauran kungiyoyin DAPPMAN da MEMAN fetur.

Kan batun karuwar farashin fetur, Mista Amoo ya ce akwai cin hanci da rashawa a sashen, wanda sai an dakile shi za a rage hauhawar farashin fetur.

Kara karanta wannan

NLC ta ja daga, ta fadi tsattsauran mataki idan aka kama shugabanta, Ajaero

IPMAN ta fadi dalilin karancin fetur

A baya mun ruwaito cewa kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN), ta bayyana dalilin da ya sa aka samu tashin farashin litar fetur zuwa sama da N900 a wasu wuraren.

Kungiyar ta bayyana cewa laifin kamfanin samar da fetur ta NNPCL ne ya sa mazauna kasar nan ke fuskantar karancin mai, inda wasu gidan man su ka rufe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.