Wani Shugaban INEC Ya Yanke Jiki Ya Faɗi, Ya Mutu Bayan Fitowa Daga Taro

Wani Shugaban INEC Ya Yanke Jiki Ya Faɗi, Ya Mutu Bayan Fitowa Daga Taro

  • Kwamishinan hukumar zaɓe ta ƙasa INEC mai kula da jihar Ogun, Niyi Ijalayeya riga mu gidan gaskiya bayan fitowa daga taro
  • Rahotanni sun nuna cewa kwamishinan ya koma masaukinsa a Otal a Abuja kafin ajali ya riske shi da ya yanke jiki ya faɗi
  • Lamarin dai ya faru ne bayan taron kwamishinonin zaɓe wanda shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya jagoranta ranar Litinin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kwamishinan hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) mai kula da jihar Ogun, Barista Niyi Ijalaye ya riga mu gidan gaskiya.

Kwamishinan wanda shi ne shugaban hukumar INEC reshen jihar Ogun ya mutu ne bayan ya yanke jiki ya faɗi da yammacin ranar Litinin a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Daga karin kumallo, uwa da ƴaƴanta 3 sun rasu a wani yanayi mai ban tausayi

Barista Niyi Ijalaye.
Kwamishinan INEC na jihar Ogun ya yanke jiki ya baɗi bayan kammala taro a Abuja Hoto: INEC Nigeria
Asali: Twitter

Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan fitowa daga taron kwamishinonin zaɓe wanda ya gudana a hedkwatar INEC karkashin jagorancin Farfesa Mahmud Yakubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Channels tv ta ruwaito cewa har kawo yanzu babu wani cikakken bayani kan musabbabin rasuwar REC na jihar Ogun.

Yadda kwamishinan INEC ya rasu

Wata majiya da ta buƙaci a sakaya sunanta ta bayyana cewa marigayin ya koma masaukinsa a otal bayan taron kafin ajali ya riske shi.

Ta ƙara da cewa Mista Niyi Ijalaye ya ba da gudummuwa a taron da aka yi har aka kammala, amma bayan ya koma otal kuma rai ya yi halinsa.

Farfesa Mahmud Yakubu ya ce taron ya maida hankali ne kan zaɓukan gwamnoni da ke tafe a jihohin Ondo da Edo da kuma na maye gurbin ƴan majalisa.

Wane taro INEC ta gudanar a Abuja?

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban INEC ya yi babban rashi da mahaifiyarsa ta rasu a Abuja

INEC ta wallafa abubuwan da aka tattauna tare da hotunan waɗanda suka halarci taron a shafinta na Facebook.

An ga Barista Niyi Ijalaye sanye da kaftani mai launin shuɗi da jar hula a ɗaya daga cikin hotunan da INEC ta wallafa a shafinta na sada zumunta bayan taron.

INEC ta tura Barista Ijalaye jihar Ogun a watan Maris din 2022 bayan ɗauke Olusegun Agbaje zuwa jihar Legas.

Mahaifiyar tsohon shugaban INEC ta rasu

Kun ji cewa Allah ya yi wa mahaifiyar tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) rasuwa a daren jiya Jumu'a, 16 ga watan Agusta, 2024

Hajiya Hauwa Kulu Muhammadu Jega ta rasu ne bayan fama da ƴar gajeruwar rashin lafiya a birnin tarayya Abuja in ji wata majiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262