Rashawa: Kashim Shettima Ya Fadi Hanyar da Tinubu Ya Kamo Domin Cafke Barayi

Rashawa: Kashim Shettima Ya Fadi Hanyar da Tinubu Ya Kamo Domin Cafke Barayi

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba za ta rika cewa uffan a kan yadda hukumomin yaki da rashawa ke gudanar da aikinsu ba
  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya bayyana haka, tare da kara cewa ya dauki matakin ba hukumomin damar ayyukansu yadda ya dace
  • Shugaba Tinubu ya ce sun lura da yadda rashawa ke taka muhimmiyar rawa wajen dakile ci gaban Najeriya, saboda haka dole a dauki mataki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa tun bayan karbar ragamar jagorancin kasar nan ya fara daukar matakin yaki da rashawa.

Kara karanta wannan

Jam'iyyun adawa sun hada kai, sun ragargaji Tinubu kan sayen sabon jirgi

Shugaban ya bayyana cewa da hawansu mulki, ya tabbatar an bayar da kudaden gudanarwa da hukumomin ke bukata domin yin ayyukansu.

Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya ce ana nasara a kan rashawa Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa haka kuma Tinubu ya ce gwamnatinsa ba ta yi wa hukumomin yaki da rashawa katsalandan kan gudanar da harkokinsu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashim Shettima ya fadi haka ne a taron shekara-shekara da cibiyar yaki da cin hanci da rashawa a Afrika ta Yamma ta shirya.

"Ana nasara kan yaki da rashawa," Tinubu

Gwamnatin Bola Tinubu ta bayyana cewa ana samun nasara a kan yaki da cin hanci da rashawa da hukumomin kasar nan ke yi da marasa kishin kasa.

Tinubu da ya bayyana haka ta bakin mataimakinsa, Kashim Shettima ya ce rashawa na daga cikin babban kalubalen da ya hana kasar nan ci gaba, Vanguard ta wallafa.

Kara karanta wannan

An zargi Gwamnatin shugaba Tinubu da satar dabarar tattalin arziki a wajen Atiku

Ya ce a matsayinsu na shugabanni, nauyi ne da ya rataya a kansu na tabbatar da an yaki cin hanci da rashawa da gaske har sai an kakkabe su daga kasar nan.

Rashawa: Tinubu ka iya sauya mukamin Ganduje

A baya mun ruwaito yadda aka samu labarin cewa alamu sun bayyana cewa zarge-zargen rashawa za su iya sa shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya rasa kujerarsa.

Ana zargin gwamnatin Tinubu ta sakawa Ganduje da mukamin jakada biyo bayan zargin almundahana, amma APC ta ce labarin ba gaskiya ba ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.