Ambaliya: Gwamnatin Kaduna Ta Bullo da Matakin Ceto Mazauna Kananan Hukumomi 7
- Mahukunta a Kaduna sun fara tsorata da yadda ake samun karuwar mamakon ruwa a yankunan jihar kwanan nan
- Zuwa yanzu, an lissafa wasu kananan hukumomi bakwai da ake fargaba su na cikin hadarin ambaliya a jihar Kaduna
- Gwamnatin Uba Sani ta ba mazauna wadannan kananan hukumomin shawarar su tattara kayansu su bar wuraren tun wuri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Gwamnatin Kaduna ta fara daukar matakan rage illar da mamakon ruwa zai haifar haifar a wasu daga cikin sassan jihar.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (KADSEMA) ta lissafa wasu daga cikin kananan hukumomi da ake fargabar ambaliya na yi masu barazana.
A sakon da KADSEMA ta wallafa a shafinta na Facebook, ta nemi mazauna yankunan su gaggauta barin wajen ganin yadda aka shafe kwanaki ana ruwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wuraren da ambaliya za ta iya shafa a Kaduna
Channels Television ta tattaro cewa gwamnatin Kaduna ta gargadi wasu yankuna kananan hukumomin jihar guda bakwai.
Daga cikin yankunan da aka nemi jama'a su bari akwai;
1. Ambaliya: Garuruwan Kaduna ta Arewa
Gwamnati ta nemi a kauracewa yankunan makarantar sakandaren Abubakar a titin Kigo, makarantar firamaren LEA Unguwan Rimi.
2. Inda za a kauracewa a Kaduna ta Kudu
Yankunan da hukumar KADSEMA ta ce na tattare da hadarin ambaliya sun hada da wurin koyon aikin hannu na Namadi Sambo da ke Tudun Wada da makarantar firamaren LEA Nassarawa.
3. Kaduna: Sauran yankunan da ke hadarin ambaliya
Sauran bangarorin da hukumar KADSEMA ta nemi a kauracewa sun hada da makarantar sakandaren Narayi a Chikun da masallacin jumaat a Hayin Malam Bello a karamar hukumar Igabi.
Sauran sun hada da firamaren LEA Agwom , firamaren LEA Tsauni da firamaren LEA a kauyen Sanga .
Sai kuma firamaren LEA Jere ta Arewa, firamaren LEA Jere ta Kudu a Kagarko da kuma GSS Kafanchan a karamar hukumar Jema’a .
Ambaliya na yin barazana ga abinci
A baya mun ruwaito cewa akwai tsoron ambaliyar ruwa a wasu jihohin Arewa zai jawo karancin abinci saboda ta'adin da mamakon ruwan sama ke yi a gonaki
Jihohin sun hada da Kano, Jigawa, Kaduna, Nasarawa, Taraba, Bauchi, Zamfara, Yobe, Sokoto da Kebbi, inda yanzu haka ake mamakin ruwan sama.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng