Gwamnan Arewa Ya Ciri Tuta, Zai Fara Biyan Ma'aikata Sabon Mafi Karancin Albashi
- Gwamnatin Adamawa za ta fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 da gwamnatin tarayya ta amince da shi
- Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya amince a fara biyan ma'aikatan jihar sabon mafi ƙarancin albashin daga watan Agustan 2024
- Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) reshen Adamawa ne ya tabbatar da hakan bayan kammala ganawa da gwamna Fintiri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya amince da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ga ma'aikatan jihar.
Gwamna Ahmadu Fintiri ya amince a fara biyan ma'aikatan sabon mafi ƙarancin albashin ne daga watan Agustan 2024.
Shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) reshen jihar Adamawa, Kwamared Emmanuel Fashe ne ya sanar da hakan bayan kammala ganawar sirri da Gwamna Fintiri a fadar gwamnati cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A baya dai Gwamna Fintiri ya yi alƙawarin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin da gwamnatin tarayya za ta amince da shi a lokacin bikin ranar ma'aikata a watan Mayun 2024.
Ma'aikatan Adamawa za su samu ƙari
A cewar Emmanuel Fashe, za a yi amfani da tsarin yin ƙari na shekarar 2019 domin lissafa sabon ƙarin da ma'aikatan za su samu a albashin su, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
Ya ƙara da cewa an umarci ofishin Akanta Janar na jihar da ya shigar da hakan a cikin albashin da za a biya na watan Agusta.
Sai dai, ma'aikatan ƙananan hukumomi za su jira sai watan Satumba kafin su samu ƙarinsu, har zuwa lokacin da hukumar albashi ta ƙasa za ta kammala aikinta.
Karanta wasu labaran kan mafi ƙarancin albashi
- Mafi karancin albashi: Jerin gwamnonin da suka ce ba za su iya biyan N70,000 ba
- Albashin N70,000: Fadan ma'aikata zai koma kan gwamnoni, za a iya rufe jihohi
- Tarihin mafi karancin albashi daga N125 zuwa N250 har ake maganar N60, 000 a yau
Gwamnatin Ondo za ta biya N70,000
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Ondo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Lucky Aiyedatiwa, ta amince da biyan N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne biyo bayan rattaɓa hannu kan ƙudirin dokar mafi ƙarancin albashin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng