Tinubu Ya Dauko Muhimmiyar Hanyar Inganta Lantarki, NERC Ta ba MTN Izini

Tinubu Ya Dauko Muhimmiyar Hanyar Inganta Lantarki, NERC Ta ba MTN Izini

  • Hukumar lura da wutar lantarki ta kasa (NERC) ta fitar da bayani kan ba wasu kamfanoni damar samar da wutar karan kansu
  • Rahotanni sun nuna cewa cikin kamfanonin da NERC ta ba izinin samar da wutar lantarki akwai kamfanin sadarwa na MTN
  • Hukumar NERC ta yi karin haske kan sharuddan da ta sanya ga kamfanonin kafin yarda musu su fara samar da wutar lantarki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta fara wani shiri domin bunkasa wutar lantarki a fadin Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan hukumar lura da wutar lantarki a Najeriya ta ba wasu kamfanoni izinin samar da wutar lantarki.

Kara karanta wannan

PDP v APC: Kotun Koli ta shirya yin hukunci a shari'ar zaben gwamna

Turken wuta
Gwamnati ta ba kamfanoni izinin samar da wuta a Najeriya. Hoto: Daniel Peter
Asali: Getty Images

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa kamfanin sadarwa na MTN na cikin waɗanda gwamantin Tinubu ta ba izinin samar da wutar lantarki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanonin da za su samar da lantarki

Punch ta wallafa cewa NERC ta bayyana cewa kamfanin sadarwa na MTN da Golden Penny Power Ltd na cikin waɗanda aka ba izini.

Haka zalika akwai kamfanin Havenhill Synergy, Auro Nigeria, Watts Exchange Limited da dai sauransu.

Yadda kamfanoni za su samar da lantarkinsu

NERC ta bayyana cewa ta ba kamfanin Golden Penny Power Ltd izinin samar da wuta ne a jihohin Legas, Oyo, Ogun da Cross Rivers.

Sai kuma kamfanin sadarwa na MTN, an ba shi damar samar da wutar lantarki ne kawai a sassan jihar Legas.

Dokokin NERC kan samar da wutar lantarki

Hukumar NERC ta bayyana cewa an ba kamfanonin izinin samar da wuta ne domin amfaninsu kawai.

Kara karanta wannan

Murna za ta koma ciki? Ambaliya ta fara barazana ga wadatar abinci

Masana na ganin hakan zai taimaka wajen rage matsalolin lantarki idan aka cigaba da ba kamfanoni izinin samar da wutar kansu.

NERC ta tura sako ga yan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa hukuma mai kula da wutar lantarki a Najeriya (NERC) ta ja kunnen yan kasa kan biyan kudi domin mallakar wasu kayan lantarki.

Rahotanni na nuni da cewa hukumar NERC ta bayyana cewa akwai kayan rarraba wutar lantarki da bai kamata ace yan Najeriya suna saye da kuɗinsu ba kwata kwata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng