'Yan Bindiga Sun Matsawa Mutane, Sun Farmaki Kananan Hukumomin Katsina

'Yan Bindiga Sun Matsawa Mutane, Sun Farmaki Kananan Hukumomin Katsina

  • Mazauna kananan hukumomi biyu a jihar Katsina sun fada mawuyacin hali bayan yan bindiga sun kai masu hari
  • An wannan karon, miyagun rike da mugayen makamai sun sace mutane biyu a Marabar Kankara a yankin Malumfashi
  • A karamar hukumar Musawa kuma, 'yan bindigar sun kwashe mutane da dama, musamman matan aure da yara kanana

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina - Miyagu sun hana mazauna kananan hukumomi biyu a jihar Katsina sakat, yayin da su ka kai hari tare da sace mata da yara.

Wannan ya jefa jama'a cikin fargabar halin da wadanda aka sace za su shiga tun bayan debe su a garin Tuge da ke karamar hukumar Musawa a jihar.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Gwamnatin Kaduna ta bullo da matakin ceton mazauna kananan hukumomi 7

Dikko Radda
Miyagu sun sace jama'a daga kananan hukumomi a Katsina Hoto: Katsina State Government
Asali: Facebook

TVC News ta wallafa cewa a harin da miyagun su ka kai Tuge, sun sace mutane da dama da har yanzu da a bayyana adadinsu ba, da su ka hada da magidanta, matan aure da kananan yara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sace mutane 2 a jihar Katsina

'Yan ta'adda sun kai hari garin Marabar Kankara a karamar hukumar Malumfashi da ke jihar Katsina inda su ka jefa jama'a cikin firgici.

Miyagun sun sace mutanen garin guda biyu, kuma zuwa yanzu ba a samu labarin sun nemi fansa ko sun kira iyalan wadanda su ka sace ba.

Rashin tsaro a jihar Katsina ya zama ruwan dare, wanda ya sanya gwamnatin Dikko Radda ta samar da hukumar tsaron sa kai ta jiha, amma har yanzu ba ta sauya zani ba.

Yan bindiga sun kashe hadimin gwamnan Katsina

Kara karanta wannan

Janye dakarun soji: 'Yan bindiga sun kwace gidajen mutane, sun fara noma a Arewa

A baya mun ruwaito cewa 'yan ta'adda sun kashe hadimin gwamnan jihar Katsina, Sanusi Ango Gyaza a gidansa da ke karamar hukumar Kankia.

Rundunar 'yan sandan jihar ta bakin kakakinta, ASP Abubakar Sadiq ta tabbatar da kisan, tare da bayyana cewa ana binciken kisan hadimin da uwargidansa.

Miyagun sun kuma yi garkuwa da amaryar marigayi Gyaza da har yanzu ba a bayyanawa jama'a halin da ake ciki ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.