Ana Fama da Yunwa, Yan Gida Daya Su 5 Sun Mutu daga Shan Miyar Gishirin Lalle

Ana Fama da Yunwa, Yan Gida Daya Su 5 Sun Mutu daga Shan Miyar Gishirin Lalle

  • An shiga jimami bayan yan gida daya sun mutum bayan cin abinci da aka yi da miyar gishirin lalle a kauyen Kaurar Wanke
  • Rahotanni sun nuna cewa mutane biyar daga cikin yan gidan sun mutu yayin da wasu biyu suke kwance a asibiti rai a hannun Allah
  • Legit ta tattauna da wata mata da ta kware a kan harkar girki domin ba mata shawara kan yadda za su kaucewa irin kuskuren wajen dafa abinci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - An shiga jimami bayan wasu yan gida daya sun mutu bayan shan miyar gishirin lalle.

Rahotanni na nuni da cewa mummunan lamarin ya auku ne a kauyen Kaurar Wanke da ke jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

"Muna bukatar taimakonka": Diyar Ado Bayero ta kuma neman alfarmar Abba Kabir

Sokoto
Yan gida daya sun mutu a Sokoto kan cin abinci mai guba. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Leadership ta wallafa cewa kwamishinar lafiya ta jihar Sokoto, Asabe Balarabe ta ziyarci wajen da abin ya faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sokoto: Yadda mutane suka sha gishirin lalle

Kwamishinar lafiya ta jihar Sokoto, Asabe Balarabe ta ce mutanen sun hada miya da gishirin lalle ne bisa kuskure.

New Telegraph ta wallafa cewa Asabe Balarabe ta bayyana cewa abin ya faru ne tun ranar Jumu'a inda wasu daga cikin yan gidan suka mutu.

Wadanda suka mutu kan shan gishirin lalle

Bincike ya tabbatar da cewa mutane uku ne yan gida daya suka mutu a ranar Jumu'ar da ta wuce kan shan miyar.

Sai kuma mutane biyu da suka mutu bayan an kai su asibitin Sokoto yayin da kwamishinar ta je duba su a ranar Lahadi.

A yanzu haka dai sauran mutane biyu na gidan suna kwance a asibiti suna karbar magani yayin da aka yi jana'izar waɗanda suka rasu.

Kara karanta wannan

An shiga jimami, tirela ta markaɗe tsohuwa da jikarta har lahira

Shugaban asibitin Sokoto ya yi magana

Shugaban asibitin Sokoto, Dakta Attahiru Isah Sokoto ya yi ishara da cewa lamarin kaddara ne daga Ubangiji.

Haka zalika Dakta Attahiru Isah Sokoto ya yi addu'a a kan Allah ya jikan wadanda suka rasu daga cikinsu.

Legit ta tattauna da Maryam Ibrahim

Wata mata da ta kware kan dafa abinci mai suna Maryam Ibrahim ta yi kira ga mata kan tabbatar da cewa sun dandana duk abin da za su saka a miya.

Maryam Ibrahim ta kara da cewa dole a rika ajiye kayan da aka san za su cutar a nesa da yara da kuma nesantar da yara daga wajen girki.

Ta bayyana cewa hakan na cikin matakan da za a dauka domin kaucewa kuskuren saka abu da zai cutar a miya.

An yi garkuwa da yan gida daya

A wani rahoton, kun ji cewa yan bindiga sun kara zafafa kai hare-hare kauyukan da ke kewaye da ƙaramar hukumar Bwari a babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Zamfara: Ana makokin Sarkin Gobir, miyagu sun kwashe mutane, an nemi fansar N50m

Karin rahotanni sun nuna cewa yan sanda biyu sun ji raunuka yayin da wasu yan bindiga suka yi garkuwa da mutum bakwai yan gida ɗaya a Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng