Sojoji Sun Cafke Shugaban Mafarauta Kan Zargin Hada Kai da 'Yan Ta'adda
- Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewa dakarunta sun cafke wani shugaban ƙungiyar mafarauta a jihar Taraba
- Sojojin sun cafke Alhaji Adamu Tanko ne bisa zarginsa da siyar da bindiga ƙirar AK-47 ga wani da ake zargin cewa ɗan ta'adda
- Bincike ya nuna cewa an gano bindigar ne bayan dakarun sojoji sun kai wani samame kan maɓoyar ƴan ta'adda a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Taraba - Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun cafke shugaban ƙungiyar mafarauta ta ƙaramar hukumar Gassol da ke jihar Taraba, Alhaji Adamu Tanko.
Dakarun sojojin sun cafke shi ne bisa zargin sayar da bindigar AK-47 ga wani da ake zargin ɗan ta’adda ne.
Sojoji sun cafke shugaban mafarauta
Rundunar sojojin ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa an gano bindigar da Alhaji Adamu Tanko ya siyar ne a jihar Plateau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar sojojin Najeriya ta fitar a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar The Punch.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Dakarun sojoji a jihar Taraba bayan samun bayanan sirri, sun cafke shugaban ƙungiyar mafarauta ta jihar Taraba, Alhaji Adamu Tanko, saboda siyar da bindiga ƙirar AK-47 ga wani da ake zargin ɗan ta'adda ne."
"Bincike ya nuna cewa an gano bindigar ne a wani samame da aka kai kan ƴan ta'adda a Boki Lamba, wani gari da ke kan iyaka da jihar Plateau."
Sojoji sun hallaka kwamandan Boko Haram
Sanarwar ta ƙara da cewa dakarun sojojin da aka tura domin yaƙi da ta'addanci a jihar Borno sun kashe Abu Rijab, wani kwamandan ƴan ta'addan Boko Haram da ke cikin jerin ƴan ta'addan da ake nema ruwa a jallo.
Sojojin sun kashe Abu Rijab da mayaƙansa ne a wani samame da suka kai musu a Bula Daloye da ke ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno.
Sojoji sun hallaka ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadarin Daji (OPHD), sun samu nasara kan ƴan bindiga a jihar Zamfara.
Jajirtattun dakarun sojojin sun hallaka ƴan bindiga biyu a ci gaba da yaƙin da suke yi da miyagu a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng