Apkabio, Barau da 'Yan Majalisa da Su ka Mallakawa Mazabunsu Ayyukan Biliyoyi

Apkabio, Barau da 'Yan Majalisa da Su ka Mallakawa Mazabunsu Ayyukan Biliyoyi

Bincike ya tono yadda shugabanni da wasu manyan wakilan yan kasar nan a majalisar dattawa su ka mallakawa kawunansu biliyoyin Naira na ayyukan mazabu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Ana raba ayyukan mazabu ga yan majalisun kasar nan 109 domin gudanar da ayyukan ci gaba a sassa daban-daban na mazabunsu.

Senate
Yan majalisu sun samu biliyoyi domin gudanar da ayyuka a mazabu Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Premium Times ta binciko yadda manyan yan majalisun su ka ba wa kawunansu ayyukan biliyoyi.Ga jerin 'yan majalisun da su ka sanyawa kansu irin wadannan ayyuka;

1. Barau Jibrin na Kano da ayyukansa

Mataimakin shugaban majalisa, Barau Jibrin ya samu ayyuka a mazabarsa na miliyoyin; har da N190m na ba masu babur tallafi a sassan Kano.

Kara karanta wannan

Abubuwa 3 da suka faru a Najeriya bayan Buhari da Jonathan sun gana da Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai N250m na samar da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana a sassan karamar hukumar Dala, N60m na gina ajujuwa a Kadawa, karamar hukumar Ungogo.

N20m kuma an ware ne domin horarwa da kuma sayo keken dinki ga mata da matasa a kananan hukumomin Gwarzo da Kabo.

2. Ali Ndume na Borno da ayyuka 3

Mazabar Sanata Ali Ndume, Borno ta Kudu ta samu ayyuka guda uku da za a yi a kan N722m.

An ware N500m domin aikin samar da hanyoyi da kwatoci a mazabar, N122m na samar da babur mai kafa uku na daukar kaya da kuma N100m na baburin adaidata sahu.

3. Abba Moro na Binuwai

Shugaban marasa rinjaye, Abba Moro mai wakiltar Binuwai ta Kudu ya samawa mazabarsa ayyuka takwas a kan N1.180bn; N200m na samar da lantarki da N50m na kammala aikin wuta.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Gwamnatin Kaduna ta bullo da matakin ceton mazauna kananan hukumomi 7

N20m na karasa aikin wuta a karamar hukumar Ogbadigbo, N500m na horar da matasa kan harkar gona, N200m na gina hanyar zamani a Ugbokolo, karamar hukumar Okpokwu.

N20m na kammala aikin wuta a Ekpemgbe da ke karamar hukumar Ado, N140m na sayo magunguna da N50m na gyara hanyoyi masu tsayin kilomita 12.

Sauran yan majalisa da kudin ayyukansu

Sauran yan majalisa da su ka mori ayyukan masu kudi sun hada da Bamidele Opeyemi na Ekiti da tsakiya da ayyuka shida akan N1.472bn.

Oyelola Ashiru na Kwara ta Kudu ya samu ayyuka 11 a kan N1.8bn, sai wakilin Osun ta Yamma, Oyewunmi Olalere ya samu ayyuka shida a kan N1.130bn.

Shugaban majalisa, Godswill Akpabio ya samu ayyukan da ya kai mazabarsa ta Arewa maso Yammacin Akwai Ibom a kan N4.142bn.

Majalisa ta yi bayani kan albashin wakilai

A baya kun ji cewa majalisar dattawan kasar nan ta yi karin bayani a kan sahihancin albashin da gwamnatin tarayya ke biyansu a duk wata.

Kara karanta wannan

Murna za ta koma ciki? Ambaliya ta fara barazana ga wadatar abinci

Dan majalisa daga Kano, Kawu Sumaila ne ya fasa kwai a kan albashin N21m da ya ce ana biyansa, sabanin N1m da hukumar raba arzikin kasa ya fada.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.