Yunwa: Marayu 5 da Mahaifiyarsu Sun Kwanta Dama a Kano
- Al'ummar Kano sun yi hutun karshen mako cikin jimami bayan da wata uwa da yaranta su ka rasa rayukansu bayan cin abinci
- Malam Yakubu Dogo Karkari, mai unguwar Karkari inda lamarin ya afku ya shaidawa Legit cewa matar ta yi tubanin da ya yi ajalinta da yaranta
- Matar ta rasu a 'ya'yanta a asibiti, inda kokarin ceto rayuwarsu ya ci tura, kuma yanzu haka jami'an tsaro za su shiga batun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Mazauna Kano sun cika da takaicin yadda wata baiwar Allah da yaranta biyar su ka rasa rayukansu a Karkari da ke Gwarzo a jihar.
Marigayiyar mai suna Alhaqatu AbdulKarim ta dafa abinci domin ba wa yaranta, inda daga nan su ka fara ciwon ciki bayan cin abinci.
Mai unguwar Karkari, Yakubu Dogo ya shaidawa Legit cewa matar ta aika a kai mata markade domin yin tubani, sai aka kawo kullin ya yi ruwa, sai ta yi amfani da dusar gero domin daureta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda yan gida daya su ka rasu
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa bayan Alhaqatu da iyalinta sun fara kukan ciwon ciki ne aka mika su babban asibiti da ke Gwarzo.
Daga nan mutum biyu su ka fara rasuwa daga ranar Talata, wasu yara biyu su ka kara rasuwa a Laraba, mahaifiyar ta rasu a Alhamis, dayan ya rasu ranar Juma'a.
Jami'an tsaro za su binciki rasuwar
Wani jami'i da ya nemi a sakaye sunansa ya tabbatarwa Legit cewa su na sa ran jami'an tsaro za su binciki lamarin domin gano ko akwai hannun wasu.
Kishiyar matar da mijinsu AbdulKarim ya rasu ya bari kimanin watanni bakwai da su ka wuce, da sauran jama'ar gidan na cikin matukar jimamin rashin.
Mata, miji, yara 5 sun rasu
A baya mun ruwaito cewa ciwon ciki sakamakon cin garin rogo ya kusan shafe wani iyali a jihar Sokoto, inda mutane bakwai su ka rasa rayukansu.
Sai dai gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa an dauki jinin mutum daya da ya tsallake rijiya da baya domin yin gwajin gano ainihin dalilin rasuwar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng