Kwanaki 3 da Dawowa Najeriya, Tinubu Zai Sake Lulawa Kasar Waje

Kwanaki 3 da Dawowa Najeriya, Tinubu Zai Sake Lulawa Kasar Waje

  • Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai kai ziyara zuwa ƙasar Faransa da ke nahiyar Turai a ranar Litinin, 19 ga watan Agustan 2024
  • Shugaba Tinubu zai dawo gida Najeriya bayan ya kammala zaman da zai yi saboda abin da ya kai shi ƙasar ta Faransa
  • Wannan ziyarar dai ita ce karo na biyu cikin mako ɗaya da Shugaba Tinubu ya shilla zuwa ƙasashen waje

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai ziyarci ƙasar Faransa da ke nahiyar Turai.

Shugaba Tinubu zai je ƙasar ne a ranar Litinin, 19 ga watan Agustan 2024 domin yin wani aiki na gajeran lokaci.

Tinubu zai tafi Faransa
Shugaba Tinubu zai kai ziyara zuwa Faransa Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Mai ba shugaban ƙasa shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya shilla kasar waje bayan dawowa hutun kwanaki 30

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe Tinubu zai dawo Najeriya?

Ajuri Ngelale ya bayyana Tinubu zai dawo ƙasar nan ne bayan ya kammala zaman da zai yi a ƙasar Faransa.

"Shugaba Bola Tinubu zai tafi ƙasar Faransa ranar Litinin, 19 ga watan Agusta, inda zai tashi daga Abuja, babban birnin ƙasar nan."
Shugaban ƙasan zai dawo gida bayan ɗan taƙaitaccen zaman aikin da zai yi a Faransa."

- Ajuri Ngelale

Sai dai, bai bayyana dalilin da ya sanya Shugaba Tinubu zai kai ziyarar ba.

Kamfanin China ya yi wa Tinubu alfarma

Sanarwar ta Ngelale ta zo ne bayan kamfanin Zhongshan Fucheng Industrial Investment Co. Limited, kamfanin ƙasar China da ya kai Najeriya gaban kotunan duniya, ya fara kawo labarin ziyarar ta Tinubu.

Kamfanin ya sanar da cewa ya saki ɗaya daga cikin jiragen shugaban ƙasan guda uku da kotu ta ba shi damar ƙwacewa saboda ziyarar da Tinubu zai kai zuwa ƙasar Faransa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fara daukar matakin tsuke bakin aljihun gwamnati

Wannan shi ne karo na biyu da Tinubu zai kai ziyara ƙasar waje cikin mako ɗaya.

Kwanaki biyu da suka gabata Shugaba Tinubu ya koma Abuja bayan ziyarar aiki ta kwanaki uku da ya kai a ƙasar Equatorial Guinea.

Tinubu ya gargaɗi jami'an gwamnati

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gargadi jami’an gwamnati da shugabannin hukumomi dangane da taron majalisar ɗinkin duniya (UNGA) karo na 79 da za a yi.

Shugaba Tinubu ya gargaɗi waɗanda ba su da wani abu da za su yi a wajen taron wanda za a yi a birnin New York na ƙasar Amurka, da kada su halarta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng