Kwangilar N8bn: Gwamnatin Kano Ta Yi Martani ga Bidiyon Dan Bello, Za Ta Fara Bincike

Kwangilar N8bn: Gwamnatin Kano Ta Yi Martani ga Bidiyon Dan Bello, Za Ta Fara Bincike

  • Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya musanta masaniyar ba kamfanin Novamed kwangilar sayowa kananan hukumomi 44 magunguna
  • Fitaccen tsohon dan jaridar nan, Dan Bello ne ya fitar da wani bidiyo da ya ke ikirarin gwamnatin Kano ta saba ka'idar ba da kwangilar
  • Gwamnatin Kano ta ba hukumar yaki da rashawa ta jihar umarnin gaggauta gudanar da bincike kan wannan zargi na badakalar N8bn

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi magana kan wani bidiyo da tsohon dan jarida, Bello Galadanchi (Dan Bello) ya wallafa awannin da suka gabata.

A cikin bidiyon, Dan Bello ya yi ikirarin cewa gwamnatin Kano ta bayar da kwangilar sayo magunguna na kusan N8bn ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Awanni da fallasa badakalar Ganduje, ‘Dan Bello ya koma kan Gwamna Abba Gida Gida

Gwamnan Kano ya yi magana kan bidiyon Dan Bello na zargin badakalar kwangila
Gwamnan Kano ya ba da umarnin gudanar da bincike kan bidiyon Dan Bello. Hoto: @BelloGaladanchi, @Kyusufabba
Asali: Twitter

Dan Bello ya saki bidiyon badakalar kwangila

Bidiyon da mazaunin kasar Sin a yanzu ya wallafa a shafinsa na X ya jawo ce-ce-ku-ce musamman daga tsagin gwamnati, da ke ganin an yi masu ba dai dai ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan Bello ya kawo wasu hujjoji da ya ce su ne suke nuna lokacin da kananan hukumomi 44 na Kano ke biyan wani kamfani N10m a kowane wata.

Tsohon ‘dan jaridar ya nuna wannan kamfani da aka ba kwangilar mai suna Novamed mallakar wani ‘dan uwan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne.

Gwamna ya yiwa Dan Bello martani

To sai dai gwamnan Kano, Abba Yusuf ya musanta masaniya kan badakalar sayen magunguna da Dan Bello ke ikirarin gwamnatinsa ta tafka.

Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan labarai, Baba Halilu Dantiye da daraktan watsa labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa.

Kara karanta wannan

Abba ya nemo alfarma ga Kanawa daga kasar waje, za a kawo shirin taimakon talaka

Sanarwar wadda shi Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook ta ce ba ta da masaniyar an ba da kwangilar sayo magunguna ga kananan hukumomi 44 na jihar.

Gwamna ya ba PCACC sabon umarni

Gwamna Abba Yusuf ya ba shugaban hukumar karbar korafe korafe da yaki da rashawa (PCACC), Muhuyi Magaji umarnin gudanar da bincike.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Gwamnan ya ba shugaban PCACC umarnin gaggauta fara bincike kan wannan zargi tare da ba da rahoton sakamakon bincike domin daukar mataki na gaba.
"Gwamna Yusuf ya yi kira ga al'ummar jihar Kano da su kwantar da hankulansu har zuwa lokacin da za a kamma bincike kan wannan badakala."

Duba sanarwar a kasa:

Murtala Garo: Mu'azu ya gaskata zargin Dan Bello

A wani labarin, mun ruwaito cewa Mu'azu Magaji, tsohon kwamishinan ayyukan na Kano ya gaskata bidiyon Dan Bello na zargin Murtala Sule Garo da karkatar da kudi.

Dan Bello ya yi ikirarin cewa tsohon kwamishinan kananan hukumomi lokacin Ganduje ya saci N10bn ya sayi kadara a birnin Makkah, zargin da Mu'azu ya gaskata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.