Kwamishinan da 'Yan Bindiga Suka Sace Kan Hanyar Zuwa Daurin Aure Ya Kubuta
- Kwamishinan matasa na jihar Anambra tare da matarsa sun shaƙi iskar ƴanci bayan ƴan bindiga sun yi garkuwa da su
- Ƴan bindigan sun sako kwamishinan ne kwana ɗaya bayan sun sace shi tare da matarsa a kan hanyarsu ta zuwa ɗaurin auren ɗiyar gwamnan jihar
- Wata majiya ta tabbatar da kuɓutar kwamishinan da iyalinsa inda ta ƙara da cewa gwamnati za ta fitar da sanarwa kan hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Anambra - Ƴan bindiga sun sako kwamishinan matasa na jihar Anambra Patrick Mba da matarsa bayan sun shafe kwana ɗaya a hannunsu.
Wani babban jami’in gwamnati wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana hakan a daren ranar Asabar.
Jami'in gwamnatin ya ƙara da cewa kwamishinan da matarsa sun shaƙi iskar ƴanci ne a ranar Asabar, 17 ga watan Agustan 2024, cewar rahoton jaridar The Punch.
"An sako kwamishinan matasa da aka yi garkuwa da shi da matarsa. Tsarki ya tabbata ga Allah. Nan ba da jimawa ba gwamnatin jihar za ta fitar da sanarwa kan hakan."
- Wata majiya
Yadda ƴan bindiga suka sace kwamishina
A ranar Juma’a ne wasu ƴan bindiga suka yi garkuwa da kwamishinan tare da matarsa, a kan hanyar Edo zuwa Kogi lokacin da suke tafiya zuwa Abuja.
Sun shirya zuwa birnin tarayya Abuja ne domin halartar ɗaurin auren Adaora, ɗiyar gwamnan jihar, Farfesa Chukwuma Soludo, wanda aka gudanar a ranar Asabar.
Rahotanni sun ce suna tafiya ne a cikin wata motar bas ƙirar Toyota Sienna ta tare da wasu fasinjoji.
An kashe ɗaya daga cikin hadiman kwamishinan wanda suke tafiyar tare da shi.
Har yanzu dai gwamnatin jihar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
Ƴan bindiga sun kashe ɗan sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kashe ɗan sanda a wani kazamin hari da suka kai shingen bincike a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.
Lamarin ya faru ne a wani shingen binciken jami'an ƴan sanda da ke ƙauyen Uruagu a ƙaramar hukumar Nnewi ta Arewa ta jihar.
Asali: Legit.ng