N16m: Bayan Kwanaki, Sheikh Gadon Kaya Ya Fadi Abin da Ya Faru da Malamai a Abuja
- Sheikh Abdullahi Usman Gadon Kaya ya rufe bakin masu zargin cewa malamai sun samu makudan miliyoyi kwanaki
- Malamai sun nemi zama da jami’an gwamnatin tarayya da aka ji labarin yarjejeniyar SAMOA, sai aka juya lamarin
- An yi ta surutu ana zargin an ba malamai N16m domin su hana zanga-zanga, Dr. Gadon Kaya ya ce duk karyar banza ce
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - An yi ta yada labari cewa gwamnatin tarayya ta rabawa malaman addinin musulunci kudi domin a rufewa al’umma baki.
An zargi malaman musulunci da karbar Naira miliyan 16 lokacin da aka yi zama da su a Aso Rock da nufin hana ayi zanga-zanga.
Hudubar Sheikh Abdullahi Usman Gadon Kaya
Sheikh Abdullahi Usman Gadon Kaya a wata huduba da ya gabatar a ranar Juma’ar nan a Gadon Kaya, ya karyata wannan zargi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Limamin kamar yadda aka ji a shafin Facebook yana jawabi a mimbari, ya bayyana cewa babu kudin da aka rabawa malamai.
Menene ya kai malamai zuwa Aso Rock?
A bayanin da ya yi, Dr. Abdullahi Usman Gadon Kaya, ya ce malamai sun je Abuja ne a kan maganar yarjejeniyar nan ta SAMOA.
Shehin yake cewa ganin gwamnatin Najeriya ta shiga wannan yarjejeniya ne aka tara malamai domin jin gaskiyar halin da ake ciki.
Gadon Kaya ya ce majalisar shari’ar addinin musulunci ta shirya taron, ya kira malamai da masana domin a zauna a Aso Rock.
Sheikh Gadon Kaya ya ce karya ake yi
A hudubar ne limamin ya karyata zargin da aka rika jifansu da shi, ya fadi har otel din da aka ajiye su na kwanakin da suka shafe.
Malamin ya ce sai sun bi layi ake raba masu abinci, kuma babu wani kudi da suka samu yayin da talakawa ke zaginsu a can gida.
Game da kudin jirgin saman da aka hau kuwa, malamin addinin ya bayyana cewa sai da suka dawo gida ne aka maida masu kudin tikiti.
A cewarsa, akwai malamin da ya kashe N300, 000 wajen sayen tikitin jirgin sama, amma a karshe sai N100, 000 kadai aka aika masa.
Wani mai suna Izala a X ya daura bidiyon, an ji Gadon Kaya yana kuka da yadda ake wulakanta malamai, ana fifita wasu mutanen banza.
Gargadi a kan wulakanta malaman musulunci
Kamar Mansur Sokoto, shehin ya jaddada cewa darajar malamai ta fi karfin a biya su N16m.
Hudubar ta soki mabiyan da ke cin mutuncin malamai, ana zarginsu da bin gwamnati duk lokacin da aka fahimci suna jin dadin rayuwa.
Saboda haka ne ya bayyana cewa yana yin noma domin samun halaliyarsa, kuma ya ba da misali da kasuwancin Sheikh Ahmad Guruntum.
Malami ya fadi kuskuren shugaba Tinubu
Dr. Bashir Aliyu Umar ya ambaci kura-kuran da Bola Tinubu ya soma da ya hau mulki a 2023 kamar yadda rahoto ya gabata a baya.
A hudubar Juma’a Sheikh Bashir Aliyu Umar, ya ci gyaran yadda aka rike bankin CBN aka jawo Naira ta yi rugu-rugu a kasuwar canji.
Asali: Legit.ng