Mafi Karancin Albashi: Jerin Gwamnonin da Suka Ce Ba Za Su Iya Biyan N70,000 Ba

Mafi Karancin Albashi: Jerin Gwamnonin da Suka Ce Ba Za Su Iya Biyan N70,000 Ba

  • Aƙalla gwamnonin jihohi biyu ne suka bayyana cewa akwai tarin matsaloli wajen aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 saboda ƙarancin kuɗi
  • Wani daga gwamnonin ya fito ƙarara ya bayyana cewa ba za iya biya ba, yayin da wani kuma ya bayyana cewa za a samu jinkiri har zuwa shekarar 2026
  • Kamfanoni masu zaman kansu masu zaman kansu sun nuna damuwarsu game da biyan sabon mafi ƙarancin albashin, inda suka buƙaci a ba su tallafi domin aiwatar da ƙarin albashin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Makonni bayan da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan ƙudirin dokar mafi ƙarancin albashi na N70,000, aƙalla gwamnonin jihohi biyu sun nuna cewa akwai matsala.

Kara karanta wannan

Shekarau ya bayyana wani babban sirrinsa kafin ya zama gwamnan Kano

Gwamnonin sun bayyana cewa akwai matsaloli wajen aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin na N70,000, saboda ƙarancin kuɗi.

Gwamnonin da ba za su iya biyan mafi karancin albashi ba
Wasu gwamnoni sun ce ba za su iya biyan mafi karancin albashi na N70,000 ba Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto
Asali: UGC

Yayin da wasu suka fito ƙarara suka bayyana gazawarsu wajen biyan karin albashin, wasu kuma ba su yanke shawara ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya

Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya ce gwamnatinsa ba za ta iya biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000 ba, saboda ƙarancin kason da take samu daga gwamnatin tarayya.

Gwamnan ya bayyana shakkun cewa wasu jihohi da dama ba za su iya biya ba, inda ya yi nuni da cewa ko aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N30,000 sai da ya nemi ya gagari wasu jihohi., cewar rahoton jaridar Leadership.

"Ba zan iya biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000 ba, kuma ina tunanin wasu jihohi da dama su ma hakan take a wajensu."

Kara karanta wannan

An kama wasu ƴan siyasa da suka ba masu zanga zanga N4bn a Abuja da jihohin Arewa 3

- Inuwa Yahaya

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba za ta fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ba har sai shekarar 2026, saboda matsalar kuɗi.

Sule ya bayyana hakan ne a wani taro da ya yi da wakilan ƙungiyoyin ƙwadago a gidan gwamnati da ke Lafia.

Gwamnan Kogi bai cimma matsaya ba

Gwamnan jihar Kogi Ahmed Usman Ododo bai fito fili ya bayyana cewa ba zai iya biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000 ba, sai dai har yanzu gwamnatinsa ba ta ɗauki wani kwakkwaran mataki ba.

A cewar rahoton jaridar The Punch, kwamishinan kuɗi na jihar Kogi, Ashiwaju Ashiru Idris, ya bayyana cewa ba a sanya ranar da za a fara aiwatar da mafi ƙarancin albashi ba.

Gwamna Abba ya kafa kwamiti

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da kwamiti kan aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata na ƙasa.

Ƙaddamar da kwamitin na zuwa ne sa’o’i 48 kacal bayan da Shugaba Bola Tinubu ya rattaɓa hannu kan dokar mafi ƙarancin albashi na N70,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng