An Ba Gwamna Abba Shawarar Korar Jami'i kan 'Karkatar' da Abincin Tallafi a Kano

An Ba Gwamna Abba Shawarar Korar Jami'i kan 'Karkatar' da Abincin Tallafi a Kano

  • An taso Shehu Wada Sagagi a gaba, ana zargin cewa ya karkatar da tallafin da gwamnatin tarayya ta turo jihar Kano
  • Mutane kamar Abdulaziz Tijjani Bako sun goyi bayan a dakatar da shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin daga aiki
  • Likitan yake cewa bai dace wanda yake jikin gwamna yana yawo da wannan zargi ba idan ana so a yaki rashin gaskiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Zargin da ake yi wa wani daga cikin manyan jami’an gwamnatin Kano na karkatar da kayan tallafi ya jawo surutu.

Jam’iyyar APC mai mulki ta na zargin an yi gaba da kayan tallafin abincin da gwamnatin tarayya ta aiko zuwa jihar Kano.

Abba Kabir Yusuf
Ana so Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dakatar da hadiminsa Hoto: Salisu Muhammad Kosawa
Asali: Facebook

An fadawa Abba ya tura Sagagi hutu

Kara karanta wannan

An binciko attajiri a gwamnatin Tinubu mai shigo da man fetur daga kasar Malta

A shafinsa na Facebook, Abdulaziz Tijjani Bako ya tofa albarkacin bakinsa game da batun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr. Abdulaziz Tijjani Bako ya na ganin bai kamata gwamnan jihar Kano ya cigaba da aiki da wanda ake yi wa wannan zargi ba.

Wanda ake zargi ya karkatar da kayan shi ne Shehu Wada Sagagi wanda tuni ya musanya wannan laifi da aka jefe shi da shi.

Abdulaziz Bako wanda babban likita ne a kasar waje, ya na cikin masu nuna goyon baya ga Kwankwasiyya a dandalin Facebook.

Gwamna Abba zai dakatar da Shehu Sagagi?

A cewarsa idan dai EFCC za ta rika tuhumar jami’in gwamnatin na Kano da rashin gaskiya, ya kamata a dakatar da shi daga aiki.

Kamar yadda ya fada, kyau Sagagi ya tafi hutu zuwa lokacin da za a kammala bincike a wanke shi ko a same shi da rashin gaskiya.

Kara karanta wannan

Sheikh Bashir Aliyu Umar: Kuskuren farko da Tinubu ya yi daga hawa mulkin Najeriya

Likitan yake cewa bai dace a rika kusantar wadanda ke da tabo ba, idan gwamnatin NNPP tana son yakar rashin gaskiya da gaske.

Dakta Bako ya yi maganar ne ganin Sagagi ya ruga kotu, ya nemo izini domin alkali ya haramtawa hukumar EFCC cafke shi.

Abdulaziz Bako a kan zargin Shehu Sagagi

“In dai gwamnatin Kano da gaske ta ke yaƙi da rashawa, idan har hukuma kamar EFCC ta tuhumi mutum da almundahana (misali yin kwana da shinkafa) to kamata ya yi gwamna ya saka shi a hutu har sai bincike ya kammala.”
“Amma ko ma dai menene, magana ta gaskiya shi ne bai kamata a ce kai matsayin da na jikin gwamna zai nemi umarnin na a hana EFCC su kama shi ba, sannan kuma ya ci gaba da zama a muƙaminsa.”
“In dai a na so gwamnati ta tafi daidai to dole ne a rufe ido a riƙa hukunta masu laifi, a kuma daina raɓar masu kashi a jika.”

Kara karanta wannan

Miyagu sun nuna karfin hali, sun kashe jami'in gwamnati kusa da gida a Nasarawa

- Abdulaziz Tijjani Bako

Wanene Shehu Wada Sagagi a siyasar Kano?

A Yunin 2023 aka ji labari Abba Yusuf ya nada Hon. Shehu Sagagi a matsayin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin na Kano.

Kafin nan ‘dan siyasar ne ya jagoranci tsagin jam’iyyar PDP da ta yaki bangaren Aminu Wali a lokacin babban zaben da ya wuce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng