Shehu Wada Sagagi ne zababben Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Kano Inji NWC

Shehu Wada Sagagi ne zababben Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Kano Inji NWC

- Ana samun sabani tsakanin Aminu Wali da Rabiu Kwankwaso a jam’iyyar PDP

- Majalisar NWC ta PDP ta tabbatar da cewa Shehu Sagagi ne shugabanta a Kano

- Uwar Jam’iyya tace an gudanar da zabe sumul, ta tabbatar da shugabannin jihar

Mun samu labari cewa uwar jam’iyyar PDP mai hamayya a kasa ta tabbatar da zaben shugabannin da aka yi kwanan nan a Kano.

A ranar 17 ga watan Disamba, 2020, shugabannin PDP na kasa, suka tabbatar da zaben da aka shirya a kananan hukumomi 44 da ke jihar.

Jam’iyyar ta bayyana haka ne a wani jawabi da ta fitar a ranar Alhamis, hakan na zuwa ne a lokacin da ake samun sabani a reshen Kano.

Jam’iyyar tace ta gamsu cewa an gudanar da zaben shugabanni na ranar 12 ga watan Disamba, 2020, ba tare da an samu wata matsala ba.

KU KARANTA: Kwankwaso ya taya PDP da Obaseki yakin zabe a Edo

Jawabin yace: “NWC ta na farin cikin sanar da cewa an shirya zabe sumul kamar yadda ka’idoji da sharudan jam’iyyar PDP su ka tanada.”

Wannan mataki da majalisar NWC ya samu daurin gindi a karkashin doka kamar yadda sashen dokar jam’iyyar na 2017 ya bada dama.

Haka zalika jam’iyyar tace hukumar INEC ta sa ido a lokacin da aka zabi sababbin shugabannin.

“Kamar yadda kuma kwamitocinmu na sauraron kara suka bada rahoto, ba a samu wani korafi ba, wanda ya tabbatar da zaben shugabannin.”

KU KARANTA: Abin da ya sa na bar kujera ta a NDDC - Kwankwaso

Shehu Wada Sagagi ne zababben Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Kano Inji NWC
Sanarwar PDP NWC kan zaben Kano Hoto: @PDPNigeria
Asali: Twitter

NWC ta ce: “Sabon shugaban jam’iyya na Kano, Shehu Wada Sagagi, zai rike kujera na tsawon shekaru hudu kamar yadda dokarmu ta tanada.”

"Uwar jam’iyyar PDP ta tabbatar da zaben sababbin shugabanni a bangaren reshenmu na jihar Kano. "inji majalisar NWC ta bakin Kola Ologbondiyan.

Idan za ku tuna, jiya ne bangaren Aminu Wali wanda su ka shiga kotu da barin Rabiu Kwankwaso, su ka kori tsohon gwamnan daga jam’iyyar.

Bangaren na Wali ya na ikirarin cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya karya wasu dokokin kundin tsarin jam'iyyar tare da shirya mata zagon-kasa a Kano.

A karshen jawabinta, jam’iyyar PDP ta yi kira ga ‘ya ‘yanta su hada kai domin ceto mutanen kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng