Tsohon Shugaban INEC Ya Yi Babban Rashi da Mahaifiyarsa Ta Rasu a Abuja
- Allah ya yi wa mahaifiyar tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) rasuwa a daren jiya Jumu'a, 16 ga watan Agusta, 2024
- Hajiya Hauwa Kulu Muhammadu Jega ta rasu ne bayan fama da ƴar gajeruwar rashin lafiya a birnin tarayya Abuja in ji wata majiya
- Wasu daga cikkn iyalan marigayyar sun tabbatar da cewa za a yi mata jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada a babban masallacin ƙasa yau Asabar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hajiya Hauwa Kulu Muhammadu Jega, mahaifiyar tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega ta rasu.
Attahiru Jega ya riƙe shugabancin hukumar zaɓe INEC daga watan Yuni, 2010 zuwa watan Yuni, 2015.
Mahaifiyar Jega ta rasu
Rahotanni sun bayyana cewa Hajiya Hauwa ta rasu ne a daren jiya Jumu'a, 16 ga watan Agusta bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a babban birnin tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya daga cikin dangin marigayyar ta tabbatar da rasuwar ga manema labarai, kamar yadda jaridar Leasership ta rahoto.
Majiya ta sanar da cewa za a yi Sallar Jana'izar marigayya Hajiya Hauwa, mahaifiyar Jega a babban Masallacin kasa yau Asabar da misalin karfe 1:30 na rana.
Ana tsammanin za a kai ta makwancin ta na ƙarshe a maƙabartar Gudu da ke birnin Abuja bayan gama Sallar janaza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Hajiya Hauwa ta rasu ta bar iyalai
An tattaro cewa Hajiya Hauwa Kulu Muhammadu Jega ta tasu ta bar ƴaƴa da jikoki da dama.
Daga cikin zuri'ar da ta rasu ta bari har da fitaccen dan jaridar nan, Malam Mahmud Jega, da tsohon Babban Darakta na AMCON, Alhaji Abbas Jega, da dai sauransu.
Jega ya magantu kan zaɓen 2023
A wani rahoton na daban Farfesa Attahiru Jega ya bayyana ra’ayinsa kan gazawa da rashin aiki na fotal ɗin nuna sakamakon zaɓe (IReV) a lokacin zaɓen 2023.
Tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ya zargi ƴan siyasa cewa suna da hannu a cikin wannan matsala.
Asali: Legit.ng