Hadimin Buhari Ya Rufewa Masoyin Ganduje Baki bayan Labarin Sace Takardun Shari'a

Hadimin Buhari Ya Rufewa Masoyin Ganduje Baki bayan Labarin Sace Takardun Shari'a

  • Bashir Ahmaad ya ba shawarar yadda za a magance matsalar da aka samu wajen shari’ar Abdullahi Umar Ganduje
  • Wasu da ake tunanin magoya bayan shugaban jam’iyyar APC na kasar ne sun tabo hadimin tsohon shugaban kasar
  • An yi musayar addu’o’i tsakanin masoya tsohon gwamnan Kano da Bashir wanda gwaninsa shi ne Muhammadu Buhari

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Jama’a su na ta maganganu a yanzu da aka sake waiwayar Abdullahi Umar Ganduje da iyalinsa da wasu zarge-zarge.

A ‘yan kwanakin nan, an hurowa shugaban jam’iyyar APC na kasa wuta har an ji labari an sace takardun shari'arsa a kotu.

Buhari da Ganduje
Magoya bayan Muhammadu Buhari da Abdullahi Ganduje sun ci karo a Twitter Hoto: @DOlusegun, @Dawisu @InsideArewa
Asali: Twitter

Ana haka ne sai Legit Hausa ta ci karo da wata tattaunawa da aka yi tsakanin Bashir Ahmaad da wani a dandalin X (Twitter).

Kara karanta wannan

Karamar magana ta zama babba yayin da APC ta tabo batun tsige Ganduje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bashir Ahmaad ya yi aiki a matsayin mai taimakawa Muhammadu Buhari a lokacin yana shugaban kasa tsakanin 2015 da 2023.

Hadimin Buhari ya yi maganar shari'ar Ganduje

Bayan gwamnan Kano ya fito ya ce an sace takardun shari’ar Abdullahi Ganduje a kotu, sai aka ji Bashir Ahmad ya ba da shawara.

Matashin ‘dan siyasar ya ce kyau a sauko da takardun da ake da su a kan na’urorin zamani domin a iya sake gabatar da hujjoji a kotu.

An taya Ganduje fada a Twitter

Daga fadan wannan sai wani Ghali Abba Abubakar ya duro, yake yi wa Bashir Ahmaad addu’ar Allah tonawa uban gidansa asiri.

A nan ne ya fada masa cewa Muhammadu Buhari ne uban gidansa kuma yana fatan a lahira zai tsira domin shi ba barawo ba ne.

"Baba Buhari ne ubangida na, shi kuma wallahi ko a lahira ba za a same shi da irin wannan laifin ba, domin kuwa shi ba barawo ba ne."

Kara karanta wannan

Sace takardun shari'a: Ganduje ya yi wa Gwamna Abba martani mai zafi

- Bashir Ahmaad

Ganduje v Buhari: Masoya sun yi musayar addu'o'i

Daga nan ne fa sai Ghali Abubakar wani matashi mai mabiya 300 ya yi masa addu’a Allah SWT ya tashe shi tare da ubangidan nasa.

Fadan hakan ya sa ya amsa da ‘Ameen’, ya kuma maida masa makamanciyar wannan addu’a.

Bashir Ahmaad wanda ya nemi takarar majalisar wakilai ya roka masa Ubangiji ya tashe shi tare da shugaban APC, Abdullahi Ganduje.

Jama’a sun taso shi a gaba ya amsa addu’ar, washegari sai aka ji ya na cewa ‘Ameen’, ya ce Dr. Ganduje ya fi Buhari ayyukan alheri.

Muhammadu Buhari sun koma Aso Rock

Rahoto ya zo cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan sun isa fadar shugaban kasa.

Sun je Aso Rock ne domin tattaunawa a zaman majalisar magabata na kasa tare da Bola Tinubu da ministoci da gwamnoni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng