Matatar Mai: Dan Jaridan da Aka Yi wa Tayin N800, 000 Ya Fallasa Masu Son Karya Dangote

Matatar Mai: Dan Jaridan da Aka Yi wa Tayin N800, 000 Ya Fallasa Masu Son Karya Dangote

  • David Hundeyin ya fasa kwai, yake cewa an tuntube shi ya yi rubutu saboda ya bata sunan matatar man Aliko Dangote
  • Dan jaridan da yake tashe ya ki amincewa da wannan tayi duk da makudan dalolin da aka yi alkawarin za a biya shi
  • A cewarsa, mafi yawan kungiyoyi na NGO na karkashin kasashen waje ne don haka sai yadda manyan duniya suka yi da su

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - David Hundeyin ‘dan jarida ne wanda ya yi suna wajen bankado bayanai da fallasa asirin manyan mutane zuwa gwamnati.

Kwanan nan aka ji matashin ‘dan jaridar ya na bayanin yadda aka yi masa tayin kudi domin ya kashewa Alhaji Aliko Dangote kasuwa.

Kara karanta wannan

Sheikh Bashir Aliyu Umar: Kuskuren farko da Tinubu ya yi daga hawa mulkin Najeriya

Dangote
Matatar man Aliko Dangote a Legas Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Cin hanci domin bata kasuwar Dangote

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na X, David Hundeyin ya ce an yi masa alkawarin $500 da nufin ya bata matatar Dangote.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, abin da ake so shi ne ya nuna cewa gina wannan matata ta na hadari ta fuskar muhallin Najeriya da dumamar yanayi.

Da aka zanta da matashin a tashar Trust TV, ya bayyana cewa bai amshi wannan tayi ba domin ya sabawa ra’ayi da irin tunaninsa.

A hirar da aka yi da shi, ya ce an tsara masa yadda zai yi rubutun da kalmomin da za a yi amfani da su sai a buga a jaridar.

Nairametrics ta ce Dialogue Earth ta Birtaniya da ke da ofishi a Kenya ta nemi ya yi rubutu, ya jero illolin matatar Aliko Dangote

Kara karanta wannan

Dattijon kasa ya fadi yadda tallafin Tinubu ke jawo karuwar talauci

Hujjar da za a fake wajen bata Dangote

Manufar rubutun shi ne a bata matatar man Dangote, a nuna cewa bai kamata a kafa matatar ba saboda yarjejeniyar COP28.

Yake cewa ana bukatar mutumin Najeriya ya yi rubutun domin attajirin nahiyar Afrikan ya fuskanci suka tun daga mahaifarsa.

“An biya kudi ana so David Hundeyin ya yi rubutu alhali ra’ayin wani mutumin Birtaniya yake da wannan tunani"
"Shiyasa na fito fili na fallasa kuma ban bata lokaci wajen sanar da kamfanin ba zan yi ba."

- David Hundeyin

Meyasa Hundeyin ya ki amsa tayin?

Ganin ana fama da matsalar makamashi a Afrika, Hundeyin ya ce bai kamata ayi amfani da shi wajen kashewa Dangote kasuwa ba.

Masu jawo dumamar yanayi su ne kasashen da suka cigaba don haka yake ganin babu abin da ya shafi Najeriya da wannan matsalar.

"Me zai hana a bar mu mu yi amfani da makamashinmu, bayan mun samu cigaba sai a fara neman wata mafitar."

Kara karanta wannan

"Ku yi hankali da yan siyasa": Sanata ya yi martani ga masarauta bayan rasa rawani

- David Hundeyin

Abin da ya sa Dangote ya tsone ido

An ji shi yana cewa ana yi wa matatar Dangote hassada ne saboda girmanta, fasahar zamanin da kuma saukin mai da za a samu.

Idan matatar ta fara aiki da kyau, ya ce za a karya wasu manyan matatu biyu a Turai

A karshe yake cewa abin takaici ana amfani da gwamnatin Najeriya, saboda wata manufa ana juya masu rike da madafan iko.

Yake cewa bai kamata a ji NUPRC tana sukar matatar Dangote, hakan zai kawo ci baya.

Yaushe Dangote zai fitar da fetur?

A kwanakin nan mu ka kawo rahoto cewa matatar man Dangote ta yi ƙarin haske kan lokacin fara fitar da man fetur zuwa kasuwa.

Matatar ta ce lokacin da aka tsara bai canza ba ganin an yi wata da watanni ana jiran man fetur ɗin a kasuwa bayan bude matatar man.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng