Shettima Ya Fadi Halin da Tinubu Ya Gaji Tattalin Arziki a Hannun Buhari

Shettima Ya Fadi Halin da Tinubu Ya Gaji Tattalin Arziki a Hannun Buhari

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta mika mata tattalin arzikin kasa a lalace
  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana haka, inda ya ce wannan ba batun siyasa ba ne
  • Sanata Shettima ya kara bukatar 'yan kasar nan da su yi watsi da surutan Atiku Abubakar da Peter Obi domin siyasa su ke

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Osun - Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa ta gaji tattalin arzikin kasa a cikin mawuyacin hali daga tsohon shugaba, Muhammadu Buhari.

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya fadi haka ne yayin kaddamar da littafi mai suna 'gano siyasar tsare-tsaren ilimin bai daya na Najeriya,'.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya tono sirri a rayuwar Tinubu, ya bar mutane da mamaki

Tinubu
Kashim Shettima ya ce a lalace su ka karbi tattalin arziki daga Buhari Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Jaridar Daily Nigerian ta tattaro Kashim Shettima na cewa duk da su 'yan jam'iyya guda ne, haka ba zai hana su fadi yadda su ka amshi mulki ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Akwai tanadi mai kyau," Shettima

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce shugaba Bola Tinubu ya yi wa 'yan kasar nan tanadi mai kyau, kuma ya na da kyakkyawar manufa.

Ya fadi haka ne a wajen kaddamar da littafin da tsohon malami, Farfesa Modupe Adelabu ya wallafa, a jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ife.

Sanata Shettima ya ce shugaba Tinubu na daukar matakan da za su farfado da tattalin arzikin, Punch ta wallafa.

Gwamnatin Tinubu ta kare tsare -tsarenta

Mataimakin shugaban kasar ya nemi 'yan kasar nan su yi watsi da kalaman tiku Abubakar da jama'ar Peter Obi.

Ya ce dukkaninsu sun shaidawa yan kasar nan cewa za su janye tallafin man fetur da daya daga cikinsu ya yi nasarar zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Dattijon Arewa ya jaddadawa Tinubu matsayarsa, Yakasai ya fadi matsalar Najeriya

Shettima ya yi mamakin talauci a Arewa

A baya kun samu labarin cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa bai kamata a ce yankin Arewacin Najeriya ta yi talauci ba.

Sanata Shettima ya ce akwai arziki jibge a yankin, saboda haka bai dace a samu mazauna yankin su ma talauci ba, kamar yadda ake gani a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.