Abba Ya Nemo Alfarma ga Kanawa daga Kasar Waje, Za a Kawo Shirin Taimakon Talaka

Abba Ya Nemo Alfarma ga Kanawa daga Kasar Waje, Za a Kawo Shirin Taimakon Talaka

  • Gwamnatin jihar Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta gana da kungiyar kasar Qatar mai ba al'umma tallafi a fadin duniya
  • Abba Kabir Yusuf ya kai ziyara ga kungiyar ne domin samar da hanyoyin yaki da talauci da inganta ilimi a Kano baki daya
  • Kungiyar ta nuna godiya ga gwamnatin Kano tare da nuna a shirye take wajen kawo dauki ga al'ummar jihar Kano a ko da yaushe

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta gana da kungiyar kasar Qatar domin nemo tallafi ga talakawa.

Abba Kabir Yusuf ya tattauna da kungiyar kan abubuwa da dama ciki har da harkar samar da ruwan sha a Kano.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun wargaza kotu a Kano, sun jawo asarar N1bn yayin zanga zanga

Abba Kabir
Abba ya nemo tallafi daga Qatar. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Daraktan yada labaran gwamnatin jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya wallafa yadda zaman Abba da kungiyar ya gudana a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayyukan da za a yi a Kano

A yayin zaman Abba Kabir Yusuf da kungiyar, gwamnan ya bukaci samar da waje da zai maida hankali kan koyar da sana'o'i da inganta ilimi.

Haka zalika Abba ko ya bukaci kungiyar ta samar da hanyoyin ba al'ummar Kano marasa karfi tallafin karatu da samar da ruwan sha ingantacce.

Idan aka samu hakan ana sa ran al'umma za su samu abin yi da wayewa wajen fuskantar rayuwa yadda ya kamata.

Samar da gidajen marayu a Kano

Haka zalika gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga kungiyar kan gina gidaje da za a yi ga marasa karfi musamman marayu.

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar Kano za ta samar da katafaren fili da za a bukata wajen gina gidajen.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun sace takardun shari’ar Ganduje a kotu lokacin zanga zanga a Kano

Martanin kungiyar Qatar ga Abba Kabir

Daraktan kungiyar Qatar a Najeriya, Elysayed Mohamed ya nuna godiya kan yadda Abba Kabir Yusuf ya kai musu ziyara.

Haka zalika Elysayed Mohamed ya yi alkawarin cewa za su ba Kano cikakkiyar kulawa kan abubuwan da gwamnan ya buƙata.

An yi asarar N1bn a kotun Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta bayyana irin asarar da ake zargi yan daba sun yi a ma'aikatar shari'ar jihar a lokacin zanga zanga.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar gani da ido ma'aikatar shari'ar Kano domin ganewa idonsa muguwar barnar da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng