Kwace Jiragen Najeriya: Kamfanin China Ya Nemi Zama da Gwamnatin Tarayya
- Har yanzu tirka-tirka tsakanin gwamnatin tarayya da wani kamfanin China yana daukar hankali bayan hukuncin kotun Faransa
- Kamfanin Zhongshan ya jawo an kwace jiragen fadar shugaban kasa da aka kai a yi wa gyaran lokaci zuwa lokaci a kasar Faransa
- Amma kamfanin Zhongshan ya yi amfani da damar wajen kwace jiragen bayan samun hukuncin kotun da ya umarci a biya sa $74.5m
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar France - Kamfanin kasar China mai suna Zhongshan ya bayyana cewa a shirye ya ke da ya tattauna da gwamnatin Najeriya wajen cimma matsaya.
Wannan na zuwa ne bayan wata kotu a Faransa ta yanke hukuncin gwamnatin Ogun ta biya kamfanin $74.5m bayan soke wata yarjejeniya da aka kulla.
Nigerian Tribune ta wallafa cewa duk da kamfanin ya ce zai iya hawa teburin tattaunawa, ya ce akwai yakinin zaman kotu da ake yi zai tabbatar masa da nasara a kan gwamnatin kasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin kasar nan ta bayyana cewa ta na aiki da gwamnatin jihar Ogun domin kare kadarorinta da ake kula da su a Faransa.
Asalin rikicin gwamnatin Ogun da Zhongshan
Premium Times ta wallafa cewa matsala tsakanin Zhongshan da gwamnatin Ogun ya samo asali ne bayan soke yarjeniyar samar da yankin cinikayya marar shinge.
Kamfanin da gwamnati sun sanya hannu a kan yarjeniyar a shekarar 2007, wanda jihar Ogun ta soke a 2015.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce kamfanin ba shi da hurumin kwace jiragen gwamnatin tarayya, domin babu ita a cikin yarjejeniyar.
Miyagu sun kama 'yan China 3 a Ogun
A baya kun ji cewa wasu 'yan asalin ƙasar China guda uku sun shiga garari bayan yan ta'adda sun yi garkuwa da su, yayin da su ke ziyarar aiki a jihar Ogun.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar a jihar, Omolola Odulola ya ce miyagun sun fara kiran waya tare da neman kudin fansa, amma ana aikin hadin gwiwa don ceto su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng