IPMAN Ta Fadi Dalilin Wahalar Mai: Litar Fetur Ta kusa N1000 a Abuja da Wasu Jihohi

IPMAN Ta Fadi Dalilin Wahalar Mai: Litar Fetur Ta kusa N1000 a Abuja da Wasu Jihohi

  • Ana ci gaba da samun matsalar samar da man fetur a fadin kasar nan wanda ya tilastawa gidajen mai da yawa dakatar da sayar da man
  • Bincike ya nuna cewa ana siyar da litar fetur daga N920 zuwa N980 a wasu gidajen mai mallakin 'yan IPMAN a Abuja da wasu jihohi
  • 'Yan kasuwar mai na kasar sun dora alhakin ƙarancin fetur da ake samu ga kamfanin NNPCL wanda suka ce ya gaza samar masu da man

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Har yanzu dai samuwar fetur ta gaza daidaita yayin da wasu 'yan kasuwar mai da dama suka rufe gidajen mansu saboda rashin kaya.

Rahotanni sun bayyana cewa farashin litar fetur ta kusa kai N1000 a wasu gidajen mai na kungiyar IPMAN da ke a garuruwan wajen birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Farashin litar man fetur ya yi tashin gwauron zabi a Kano

IPMAN ta yi magana yayin da farashin litar fetur ke shirin kaiwa N1000
Farashin litar fetur na shirin kaiwa N1000 a Abuja da waus jihohi, IPMAN ta yi magana. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

IPMAN ta yi magana kan karancin mai

Jaridar Daily Trust ta ce masu ababen hawa na shafe awanni suna layi a gidajen man kamfanin NNPCL da wasu gidajen man IPMAN da suke aiki a birnin Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan kasuwar mai na kasar sun dora alhakin ƙarancin man da ake samu ga kamfanin NNPCL wanda suka ce ya gaza samar masu da man.

Da yake magana da manema labarai, shugaban IPMAN na Ejigbo, Legas, Akin Akinade ya ce:

"Ba ma samun mai kai tsaye daga NNPC. Muna saye ne daga wurin 'yan kungiyar DAPMAN, wanda farashinsu ya bambanta da na gwamnati."

Wahalar fetur ta tsananta a birnin Abuja

Rahoto ya nuna cewa an rufe gidajen mai da dama a Abuja yayin da layi ya yi yawa a gidajen da ke bude.

An ce gidan man Ngelzarma da ke Lokogoma, gundumar Kabusa, na sayar da litar fetur din a kan N980.

Kara karanta wannan

Jigawa: Wasu matasa 2 sun mutu a yanayi mai ban tausayi a hanyar zuwa Kasuwa

Shi kuma gidan man Christees da ke a Lokogoma na sayar da lita a kan N950, yayin da gidajen NNPCL ke sayarwa a kan N617, lamarin da ya haddasa dogon layi.

Farashin litar man fetur a Kaduna

Ko da muka tuntubi shugaban gidan man Shade da ke Igabi, Kaduna, ya ce suna sayar da lita a kan N900 amma a halin yanzu babu man.

Wani direban mota, Mallam Salim ya ce ya sha mai a wani gidan mai Rugoji da ke sha-tale-talen Nnamdi Azikwe, Kaduna, a kan N920 a ranar Alhamis.

Gidajen mai da dama sun daina bayar da mai a sassan jihar sakamakon ƙarancin man da ake fama da shi, inda shi ma gidan NNPC na hanyar Abuja ya ke a rufe.

N950: Fetur ya yi tsada a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa farashin litar fetur ya yi tashin gwauron zabi a jihar Kano, inda ake sayar da litar a kan N950 zuwa N980.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fada hannun ƴan damfara, ana tura sakon neman kudi a lambarsa ta WhatsApp

Sai dai an ce akwai gidajen man da farashinsu bai kai hakan ba, duk da cewa ba su da yawa amma dai ana samun dogon layin ababen hawa.

Wannan na zuwa ne yayin da aka kammala zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa wanda aka shafe kwanaki 10 ana yi a kusan fadin kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.