An Shiga Fargaba a Kano, NEMA Ta Lissafa Garuruwan da ke Fuskantar Hadarin Ambaliya
- Kimanin garuruwa 362 daga kananan hukumomi 14 na jihar Kano ne ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a daminar 2024
- Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, ta yi gargadin cewa ambaliyar za ta iya shafar kusan mutane miliyan 4 a jihar
- Shugabar hukumar NEMA, Misis Zubaida Umar ta ce zubar da shara a magudanun ruwa na daga cikin dalilan ta'azzarar ambaliya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, ta yi gargadin cewa garuruwa 362 daga kananan hukumomi 14 na jihar Kano na fuskantar hadarin ambaliya.
Shugabar hukumar NEMA, Misis Zubaida Umar, ta bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki na kwana daya da aka yi a Kano ranar Alhamis.
Garuruwan Kano da ke fuskantar ambaliya
Jaridar Daily Trust ta ruwaito taken taron shi ne: "Karfafa juriyar al'umma ta hanyar gudanar da magance matsalar shara da kiyaye ambaliya"
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Misis Zainab wanda ta samu wakilcin Dakta Nuraddeen Abdullahi, jagoran NEMA na Kano, ya ce hukumar kula da ruwa ta Najeriya (NIHSA) AFO ta yi hasashen mutane 3,749,200 na fuskantar hadarin ambaliyar ruwa a jihar.
Ta lissafa kananan hukumomin 14 da suka hada da: Rimin Gado, Tofa, Kabo, Madobi, Garun Malam, Bebeji, Rano, Dawakin Kudu, Warawa, Wudil, Sumaila, Ajingi, Kura da Dala.
Ambaliya: NEMA ta fadi matakan kare kai
Misis Zubaida ta ce an yi taron ne da nufin aiwatar da ingantattun matakan wuri da za su kare rayuka da dukiyoyin jama'a a lokacin damina, inji rahoton The Punch.
"Ambaliyar ruwa a shekarar 2012 da 2022 ta nuna mahimmancin buƙatar haɗin kai a dukkanin matakan gwamnati domin magance haɗarin ambaliyar.
"Sau da dama Kano na fuskanci ambaliyar ruwa, kuma hasashe ya nuna cewa wasu yankunan za su sake fuskantar kalubalen, musamman saboda zubar da shara a cikin magudanun ruwa.”
- Shugabar NEMA
Shugabar ta jaddada bukatar hada kai dom wayar da kan jama’a kan yadda ake sarrafa sharar gida da kuma dakile hadurran ambaliyar ruwa daga matakin farko.
Ambaliya: Gidaje sun ruguje a Jigawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa mazauna garin Gantsa a karamar hukumar Buji da ke Jigawa sun fara gudun tsira bayan ambaliyar ruwa ta barke a yankin.
Zuwa yanzu an tabbatar da rushewar gidajen jama'a sama da 100, yayin da mamakon ruwan sama ya mamaye garin saboda rashin hanyar da ruwan zai wuce.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng