Mutane 26 sun rasu, gidaje 1000 sun lalace a sanadiyyar ambaliyar ruwa a Kano
- Akalla mutane 26 sun riga mu gidan gaskiya gidaje 1000 sun lalace a sanadiyyar ambaliyyar ruwa a Kano
- Sakataren hukumar taimakon gaggawa na jihar ne ya tabbatar da adadin a wani tattaunawa da NAN
- Kananan hukumomin da abin ya shafa sune Bunkure, Minjibir, Tarauni da Doguwa
Hukumar taimakon gaggawa ta jihar Kano, SEMA, ta bayyana ranar juma'a cewa akalla mutane 26 sun rasa rayuwarsu, gidaje 1000 sun lalace a wasu kananan hukumomi 4 a jihar sakamakon ambaliyar ruwa daga watan Afrilu zuwa yanzu.
Sakataren Hukumar ta Kano, Dr Saleh Jili ne ya tabbatar da adadin a wani tattaunawa da kamfanin dillancin labarai a Kano, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
Jili yace wasu mutane hamsin sun samu raunika a sanadiyyar ambaliyar da iska mai karfi.
Yace kananan hukumomin da abin ya shafa sune Bunkure, Minjibir, Tarauni da Doguwa.
Hukumar ayyukan ruwan Nijeria, NiMet, ta bayyana a baya cewa za'ayi ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 25 a fadin jihar wannan shekarar.
Shugaban hukumar SEMA yace hukumar ta ziyarci wadanda abin ya shafa a madadin gwamnatin jihar kuma sun kai musu kayayyaki da zai rage musu radadin al'amarin.
Yace:
"Abubuwan da muka kai musu sun hada da siminti, buhunan shinkafa, masara,gero, da sabulai,"
Sakateran ya yabawa gwamna Abdullahi Ganduje da kwamishinan muhimman ayyuka, Muntari Ishaq akan taimakon kungiyar.
Ina shawarta da a agazawa wadanda abin ya afka musu
Yayi kira da hukumomin agaji da masu hannu da shuni akan su taimakawa mutanen da abin ya fada musu.
Yace:
"Tattalin arzikin mu yayi kasa a sanadiyyar korona, gwamnati bazata iya ita kadai ba,".
Ya kara kira ga wadanda suke rayuwa a kusa da rafika a jihar dasu tashi daga wurin su koma wani wuri akalla na tsawon watanni biyu.
"Idan rafika sun cika a inda kuke zama ya kamata ku kaurace wa wurin,"A cewarshi.
Ya kuma shawarci mazauna jihar dasu gyara magudanar ruwan gaban gidajensu domin tsari daga ambaliyar ruwa.
"Ina shawartar wadanda ambaliyar ruwan bata shafa ba dasuyi iya yinsu su gyara magudanar ruwa, da kuma zubar da shara a inda ya kamata domin kauracewa ambaliyar ruwan,"Ya kara.
Jili ya kara da cewa hukumar bazata gaza ba wurin ganin cewa ta tsare rayuka da dukiyoyin mutane.
Yan Najeriya su shiryawa mumunan ambaliyar ruwan sama
Hukumar ayyukan ruwan Najeriya (NIHSA) ta yi hasashen cewa tsakanin watan Agusta da farkon Oktoba, za'ayi mumunan ambaliyan ruwan sama a Najeriya.
NIHSA tace ambaliyar zata munana a wasu jihohi da birnin tarayya Abuja, rahoton DT.
Dirakta Janar na hukumar, Injiniya Nze Clement Onyeaso, a hirar da yayi da manema labarai a Abuja, ya ce dukkan jihohin da aka ambata a farkon shekara zasu fuskanci ambaliya su shirya.
Ya yi kira ga yan Najeriya su shiryawa wannan ambaliya ta hanyar gyara magudanun ruwa tare da cire bola, ciyayi, gansakuka dss.
Asali: Legit.ng