EFCC: Tsohon Gwamnan CBN Ya sake Shiga Matsala, Kotu Ta Kwace $2.04m da Kadarori
- An umurci tsohon gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele da ya janye ikon mallakar $2,045,000 da aka alakanta su da shi
- Akintayo Aluko na babbar kotun tarayya ne ya bayar da wannan umarni, inda ya kara da cewa ana zargin kudaden na haram ne
- Kotun ta kuma bayar da umarnin kwace wasu kadarori bakwai na wucin gadi da hannayen jarin tsohon gwamnan babban bankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta ba da umarnin a kwace $2,04m na wucin gadi da aka alakantawa da Godwin Emefiele, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN.
Mai shari’a Akintayo Aluko na kotun ya kuma bayar da umarnin cewa tsohon gwamnan na CBN ya bata satifiket biyu na wasu hannayen jari guda biyu da ke a kamfanin Queensdorf Global Fund.
Kadarorin Godwin Emefiele da aka kwace
Bugu da kari, kotun ta ba da umarnin kwace wasu kadarori bakwai na wucin gadi da da ke da alaka da Emefiele, inji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga jerin kadarorin kamar haka:
- Gidaje biyu masu bangarori biyu a unguwar Lekki Phase 1, Legas
- Filin da ba a gina shi ba a Ikoyi, Legas
- Gida guda daya a Ikoyi, Legas
- Gida mai dakuna hudu a Ikoyi, Legas
- Wani rukunin masana'antu da ake ginawa a Agbor, jihar Delta
- Rukunin gidaje takwas a Ikoyi, Legas
- Katafaren gida a Ikoyi, Legas
Kotu ta fadi dalilin kwace kadarorin Emefiele
Mai shari’a Akintayo Aluko ya bayar da umarnin kwace kadarori, kudi da hannayen jarin na wucin gadi bayan da lauyan hukumar EFCC, Rotimi Oyedepo, ya gabatar da bukatar da Idi Musa, mai binciken EFCC ya goyi baya.
The Punch ta ruwaito takardar bukatar ta yi zargin cewa Emefiele da mukarrabansa sun samu kadarori da kudaden ne ta hanyar wasu ayyuka da suka sabawa doka.
Umurnin kotun ya yi dai dai da sashe na 17 na dokar zamba da sauran laifuffukan da suka shafi zamba mai lamba 14, 2006, da kuma hurumin kotun.
Kotu ta hana Emefiele fita waje
A wani labarin, mun ruwaito cewa babbar kotun tarayya dake zama a Maitama a Abuja, ta hana tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele zuwa Ingila.
Tsohon gwamnan babban bankin ya kasa bayyana shaida da ke tabbatar da cewa an gayyacesa zuwa asibiti ne kamar yadda yayi ikirari tun farko.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng